Ramadan: Umarnin da Saudiyya Ta ba Al'ummar Musulmi game da Duba Jinjirin Wata

Ramadan: Umarnin da Saudiyya Ta ba Al'ummar Musulmi game da Duba Jinjirin Wata

  • Hukumomi a Saudiyya sun fara fitar da sanarwa yayin da aka fara jin kamshin watan Ramadan ta shekarar 2026
  • Kotun Koli ta Ƙasar Saudiyya ta bukaci Musulmai su fara duba jinjirin Ramadan a yammacin Talata, 29 Sha’aban 1447H
  • Sanarwar ta ce ranar ta yi daidai da 17 ga Fabrairu, 2026, bisa kalandar Umm Al-Qura da ake amfani da ita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun fitar da sanarwa game da duba watan Ramadan da ke shirin kamawa.

Kotun Koli ta Ƙasar Saudiyya ta yi kira ga daukacin Musulmai a fadin masarautar su fita domin duba jinjirin watan Ramadan.

An sanar da ranar duba wata a Ramadan
Musulmai a Saudiyya na kallon sararin samaniya don duba jinjirin watan Ramadan a Kudu maso Yammacin birnin Taif. Hoto: Allen Chen, AMER HILABI via Getty Images.
Source: Getty Images

Umarnin Saudiyya da ba Musulmi kan duna wata

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin Inside the Haramain ya wallafa a X a yau Lahadi 15 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gidan limamin masallacin Izala da dare, sun sace iyalansa

An bayyana cewa za a gudanar da binciken ne a yammacin ranar Talata, 29 ga Sha’aban 1447 Hijiriyya.

Ranar ta yi daidai da 17 ga watan Fabrairu, shekarar 2026, kamar yadda kalandar Umm Al-Qura ta nuna.

Haka kuma, kotun ta bukaci duk wanda ya ga jinjirin da ido tsirara ko ta hanyar na’urar hangen nesa ya kai rahoto kotu.

An ba da umarni kan duba watan Ramadan a Saudiyya
Al'ummar Musulmi na duba watan azumin Ramadan a Saudiyya. Hoto: @Insharifain.
Source: Twitter

Tsarin yadda za a sanar da ganin wata

An ce ana son masu gani su tuntubi kotu mafi kusa da su domin su yi rajistar shaidarsu da ganin wata cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce:

"Kotun Koli ta Ƙasar Saudi Arabia ta yi kira ga dukkan Musulmai a fadin masarautar da su fita domin binciken ganin jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 ga Sha’aban 1447 Hijiriyya bisa kalandar Umm Al-Qura wanda ya yi daidai da 17 ga Fabrairu, 2026.
" An bukaci duk wanda ya ga jinjirin da ido tsirara ko ta hanyar na’urar hangen nesa da ya tuntubi kotu mafi kusa domin yin rajistar shaidarsa."

Kara karanta wannan

Australia: An sanar da ranar da musulamai zasu fara azumin Ramadan na 2026

Kotun Koli ta kuma bayyana fatan cewa duk wadanda suke da damar bibiyar ganin jinjirin za su ba da muhimmanci ga wannan al’amari.

Ta bukace su da su shiga kwamitocin da aka kafa a yankuna domin wannan aiki na duba jinjirin watan.

Haka kuma, ta karfafa musu gwiwa su nemi lada da sakamako ta hanyar halartar wannan aiki da zai zama alheri a garinsu.

An jaddada cewa hakan na kunshe da hadin kai a kan ayyukan alheri da takawa, kuma yana amfanar daukacin al’ummar Musulmi baki daya.

Saudiyya ta fadi ranar duba watan Ramadan

Mun ba ku labarin cewa kasar Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.

Idan har an ga watan a ranar Talata, to za a fara azumin Ramadan ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, kamar yadda sanarwa ta nuna.

Idan ba a ga watan ba, to watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan a fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, 19 ga watan na Fabrairun 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.