Bayan Janye 'Yan Sanda daga Gadin Manya, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Inda Ta Kai Su

Bayan Janye 'Yan Sanda daga Gadin Manya, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Inda Ta Kai Su

  • Gwamnatin tarayya ta ba da karin bayani kan kokarin da take yi wajen samar da tsaro a sassa daban-daban na kasar nan
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa ana samun ci gaba wajen samar da tsaro
  • Ya bayyana yadda rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi da jami'an da aka janye daga gadin manya a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa rundunar yan sandan Najeriya (NPF) ta gudanar da gagarumin sauye-sauye kan jami’an da a baya aka ware don kare manyan mutane.

A cewar ministan, an tura waɗannan jami’an da aka janye zuwa al’ummomin da ke jihohin Kwara, Plateau, Benue, Kogi, Nasarawa, Neja, da kuma babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da “muhimman ayyukan sintiri na kare al’umma”.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

An tura 'yan sandan da aka janye daga gadin manya wajen samar da tsaro
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun 2026.

'Yan sanda na daukar matakan tsaurara tsaro

Ya ce wannan sauyin yana daga cikin tsaurara matakan tsaro a karkashin shirin nan mai suna "Operation Savannah Shield", wanda ke da nufin kare al’ummomin da ke fuskantar barazana a shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Wannan ya biyo bayan hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan, ciki har da wanda ya faru a jihar Kwara wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 75.

Mohammed Idris ya bayyana cewa waɗannan sababbin matakan sun haɗa da inganta tattara bayanan sirri, tura dakarun gaggawa, da kuma kara yawan jami’an tsaro a kusa da wuraren ibada.

Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasa ya sake jaddada cewa ayyukan yaki da ta’addanci a Najeriya za su kasance karkashin jagorancin kasar nan ne kacokan.

Kara karanta wannan

Yunkurin kama El Rufai, lauyoyi sun zayyana dokoki 5 da jami'an tsaro suka take

Ya ce ana maraba da haɗin gwiwar kasashen duniya ta fuskar bayanan sirri da sa ido daga abokan haɗin gwiwa kamar Amurka.

Ina aka kai 'yan sandan da aka janye?

“Tare da kara yawan jami’an tsaro da ake yi a halin yanzu a al’ummomin da ke fuskantar barazana, Shugaba Tinubu yana nuna jajircewa wajen kare rayukan ƴan Najeriya da kuma kiyaye hakkin kowane ɗan ƙasa na yin ibada cikin ƴanci."
“Ana aiwatar da ingantaccen tsaro a kusa da wuraren ibada, gami da kara yawan jami’ai a kusa da majami’u ranakun Lahadi, cikin haɗin gwiwa da shugabannin al’umma da na addini."
“Domin kara karfafa tsarin tsaro, rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da gagarumin sauyin jami’an da a baya aka tura wajen rakiya da kare manyan mutane a faɗin ƙasar nan."
“An mayar da waɗannan jami’an zuwa muhimman ayyukan sintiri na kare al’umma, wanda hakan ya samar da gagarumin ci gaba a fannin tsaro a jihohin Kwara, Plateau, Benue, Kogi, Nasarawa, Neja, da babban birnin tarayya Abuja."

- Mohammed Idris

An tura 'yan sanda don samar da tsaro
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

'Yan sanda za su yi ritaya a 2026

Kara karanta wannan

Rana ta baci: An kama 'yan fashi dauke da kayan satan miliyoyin Naira a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya za su yi ritaya a shekarar 2026.

Hukumar kula da fanshon 'yan sanda ta bayyana cewa fiye da jami’ai 5,000 ake sa ran za su yi ritaya daga aiki a shekarar 2026.

Jami'an 'yan sandan dai za su yi ritaya ne bayan sun kwashe shekaru suna hidimtawa kasar nan wajen samar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng