Ana Neman Sauke Amupitan, INEC Ta Gabatar da Kasafin Kudin N873bn don Zaben 2027
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara shirye-shiryen gudanar da babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya gabatar da bukatar kasafin kudin da hukumar ke nema don gudanar da zaben 2027
- Hukumar INEC ta raba kasafin kudin na Naira biliyan 873.78 zuwa muhimman bangarori guda hudu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gabatar da bukatar kasafin kudi don gudanar da zaben shekarar 2027.
Hukumar INEC ta gabatar da bukatar kasafin kudi na jimillar naira biliyan 873.78 domin gudanar da babban zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya gabatar da kasafin a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan al’amuran zabe a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2027.
INEC ta ware kudaden da take so don zaben 2027
Hukumar INEC ta ware kaso mai tsoka ga ayyukan zabe, fasahar zamani, da kuma manyan ayyuka.
Farfesa Joash Amupitan ya bayyana shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027 sun riga sun kankama.
Ya bayyana cewa hakan ya yi daidai da tanadin doka wanda ya wajabta cewa dole ne a amince da kudaden zabe a kalla kwanaki 360 kafin ranar da aka kayyade don gudanar da zaben, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Zaman kare kasafin kudin kwamitin ya kasance karkashin jagorancin Sanata Simon Bako Lalong da takwaransa na majalisar wakilai, Hon. Adebayo Balogun.
Ya bayyana cewa amincewa da kasafin kudin da wuri yana da muhimmanci domin tabbatar da tsari mai kyau da kuma gudanar da zabubbukan a fadin kasa ba tare da wata tangarda ba.
Yadda INEC za ta kashe kudaden
Bisa taƙaitaccen bayanin da aka gabatar, Hukumar ta raba kasafin kudin gida hudu:
- Ayyukan zabe ya samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 375.75, wanda zai kunshi ayyukan da suka shafi gudanar da zabubbukan kai-tsaye.
- An ware N92.31bn a matsayin kudaden gudanarwa a kasafin kudin.
- Bangaren fasahar zabe ya samu Naira biliyan 209.21, wanda ke nuna yadda hukumar ke ci gaba da dogara ga tsarin amfani da fasahar zamani.
- Hakazalika, hukumar INEC ta bukaci naira biliyan 154.90 domin gudanar da manyan ayyuka.
Idan aka hada wadannan manyan rukuni hudu, jimillar kudin ta kama Naira biliyan 832.17.

Source: Facebook
Amupitan ya bayyana cewa an ware karin naira biliyan 41.61 domin wasu abubuwan na daban, wanda hakan ya sanya jimillar kudaden da ake nema domin babban zaben 2027 ta kai Naira biliyan 873.78.
INEC ta yi rajistar sababbin jam'iyyu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta yi rajistar wasu sababbin jam'iyyu.
Hukumar INEC ta yi rajista ga sababbin jam’iyyun siyasa guda biyu daga cikin wadanda suka nemi bukatar hakan a wajenta.
Sab Sababbin jam’iyyun da hukumar INEC ta yi wa rajista su ne: Democratic Leadership Alliance (DLA) da Nigeria Democratic Congress (NDC)
Asali: Legit.ng

