Dokar Zabe: Amaechi Ya Tafi da Dansa wajen Zanga Zanga a Majalisar Dattawa, Ya Fadi Dalili
- Ana ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da matakin da majalisar dattawa ra dauka na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanar gizo
- Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya zama babban jigon jam'iyyar ADC na biyu da ya halarci wurin zanga-zangar
- Rotimi Amaechi ya halarci zanga-zangar ne tare da babban dansa domin nuna adawa da matakin na majalisar dattawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da babban dansa, sun halarci majalisar tarayya domin gudanar da zanga-zanga.
Rotimi Amaechi da dan nasa sun je wurin ne don halartar zanga-zangar nuna rashin yarda da matakin da Sanatoci suka dauka na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai-tsaye ta yanar gizo.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Amaechi ya je wurin zanga-zangar ne a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026.
Jagororin ADC sun shiga zanga-zanga
Amaechi shi ne jigo na biyu a jam’iyyar ADC da ya shiga wannan zanga-zangar ta neman amincewa da tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanar gizo.
A ranar Litinin ma, Peter Obi, daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin ADC, ya halarci zanga-zangar, inda ya yi kira ga majalisar tarayya da ta amince da tura sakamakon zabe kai-tsaye.
Me Amaechi ya ce a wajen zanga-zanga?
Da yake jawabi a wurin zanga-zangar a ranar Talata, Amaechi ya bayyana cewa ya bukaci dansa, wanda likita ne, da ya shiga zanga-zangar domin ya taimaka wa masu zanga-zangar da ke bukatar kulawar likita.
“Akwai wadanda ke cewa mu ‘yan siyasa muna son zanga-zanga amma ’ya’yanmu suna kasashen waje. To ga babban dana nan. Shi likita ne; na zo da shi nan kuma aikinsa shi ne idan aka samu rauni, ya duba mutane.”
- Rotimi Amaechi.
Amaechi ya kara da cewa ya kamata shugabanni su kasance a sahun gaba a manyan zanga-zanga kuma su kasance a shirye su saka iyalansu a ciki, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Amaechi ya zargi APC
Game da babban dalilin zanga-zangar, dan siyasar ya ce tsohuwar jam’iyyarsa APC, tana adawa da tura sakamakon zabe ta hanyar fasahar zamani ne saboda tana tsoron faduwa zabe.

Source: Twitter
“Na yi amanna cewa ya kamata jam’iyyun hamayya su fito, PDP, ADC, kowa ya fito domin yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da kokarin da wata jam’iyya guda daya take yi.”
"Idan muka fito, sai su ce ’yan hamayya sun kwace zanga-zangar, to su APC me suke yi? Shin su ba kwacewa suke yi ba? Me suke tsoro?”
Amaechi ya jaddada cewa jam’iyyun hamayya da kungiyoyin farar hula za su ci gaba da zanga-zangar, koda kuwa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Shugaba Bola Tinubu sun ki saurarensu.
Amaechi ya fadi kuskuren 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya dora gazawar sauya gwamnati kan 'yan adawa.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa matsalolin zaɓe da Najeriya ke fuskanta ba wai saboda rinjayen masu mulki ba ne, illa gazawar jam’iyyun adawa.
Ya ce jam’iyyun adawa sun shagaltu da lissafin kabilanci da na yankuna wajen rabon mulki, maimakon tattaunawa kan kyakkyawan shugabanci da farfaɗo da ƙasa.
Asali: Legit.ng

