Dangote: Abin da zai Ɗaga Farashin Litar Man Fetur zuwa N1000
- Matatar Dangote ta ce dogaro da jigilar man fetur ta teku na iya tura farashin lita zuwa kusan N1,000 a gidajen mai
- Babban kamfanin ya yi gargadin cewa tsarin higilar man fetur daga bakin teku na iya ƙara N1.75tr a duk shekara
- Matatar ta jaddada cewa jigilar man fetur ta hanyar amfani da tanka daga wurin dauko mai ce mafi araha da inganci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Matatar Dangote ta yi gargadin cewa dogaro da jigilar man fetur ta bakin teku na iya haifar da ƙarin kuɗIn jigilar man fetur zuwa gidajen mai.
Matatar ta bayyana cewa idan aka dogara da wancan tsari, za a iya tilasta kara farashin litar man fetur zuwa N1000.

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa dakon kayan daga taku da ake kira 'coastal logistics' na nufin safarar kayayyaki, musamman man fetur da makamantansu, ta hanyar jiragen ruwa a bakin teku maimakon amfani da bututun mai ko tituna.
Dangote ya yi gargadi kan farashin mai
Jaridar Punch ta wallafa cewa tatatar ta bayyana cewa duk da ‘yan kasuwa suna da ‘yancin zaɓar hanyar da za su fitar da mai, wannan tsarin na iya jawo tsadar kaya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, matatar ta ce dogaro da jigilar man fetur ta teku, musamman a cikin jihar Legas, zai jawo yawan kudin da zai shafi farashin litar mai.

Source: Getty Images
A ra'ayin matatar, jigilar man fetur ta teku na iya ƙara kimanin N75 kan kowace lita. Idan aka dora wannan ƙarin kuɗi a kan masu amfani, hakan na iya tura farashin zuwa N1000 a gidajen mai.
Dangote ya buga lissafi kan tsadar mai

Kara karanta wannan
Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya
Matatar Dangote ta ce ana amfani da man fetur a Najeriya na kusan lita miliyan 50 a rana da kuma lita miliyan 14 na dizal.
Matatar ta kiyasta cewa ci gaba da dogaro da dakon mai ta teku zai iya haifar da ƙarin kuɗi kusan N1.752tr a duk shekara.
Matatar na ganin dole ne a fanshe wannan kari da za a samu ko a kan masu sayen fetur ko kuma masu sayo wa.
Matatar ta sake jaddada ƙudirinta na samar da ingantattun kayayyakin man fetur a farashi mai rahusa domin kowa ya mora,
Ta bukaci ‘yan kasuwa da masu masu ruwa da tsagi a harkar da su rungumi hanyoyin jigilar da za su tabbatar da daidaiton farashi mai da kare walwalar jama’a.
Farashin man fetur na shirin tashi
A baya, kun ji cewa ana ci gaba da nuna damuwa a Najeriya cewa farashin fetur na iya kaiwa N1,000 kan kowace lita nan gaba kaɗan, sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin ’yan kasuwar man fetur, waɗanda suka ce hauhawar farashin danyen mai a duniya na da tasiri kai tsaye kan farashin man da ake sayarwa a cikin gida.
Sun bayyana cewa duk wani sauyi a kasuwar duniya kan shafi farashin fetur a Najeriya, musamman a wannan lokaci da ake fama da canje-canjen tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
