Masu Ibada da Aka Sace a Kaduna, Sun Fadi Yadda Rayuwa Ta Kasance a hannun 'Yan Bindiga

Masu Ibada da Aka Sace a Kaduna, Sun Fadi Yadda Rayuwa Ta Kasance a hannun 'Yan Bindiga

  • Wasu masu ibada da 'yan bindiga suka sace a jihar Kaduna, sun shaki iskar 'yanci bayan kwashe kwanaki a cikin daji
  • Mutanen da suka tsira daga hannun 'yan bindigan, sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a tsawon kwanakin da suka kwashe
  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Mutanen da suka tsira daga hannun 'yan bindigan da suka sace su a kauyen Kurmin Wali, da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun bayyana irin wahalar da suka sha.

Mutanen da suka tsiran sun bayyana cewa sun rayu ne da garin masara da aka haɗa da ruwa, tare da kwana a cikin daji a tsawon makonni.

Kara karanta wannan

Mutanen da aka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna sun bar hannun 'yan bindiga

Mutanen da suka tsira daga hannun 'yan bindiga sun yi bayani
Gwamna Uba Sani tare da wasu daga cikin mutanen da aka sace a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wadanda abin ya shafa sun ba da labarin ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026 bayan da Gwamna Uba Sani ya karɓe su a Gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.

Wane hali suka shiga a hannun 'yan bindiga?

Wata mace daga cikin waɗanda suka tsira, wadda ta nemi a ɓoye sunanta yayin da take rungume da jaririnta, ta ce masu garkuwar sun ba su abinci sau huɗu kacal a tsawon lokacin da suka yi a cikin dajin.

"Sun ciyar da mu da garin masara ba a dafa ba sau huɗu kacal. Muna haɗa shi da ruwa domin mu samu abin da za mu sanya a ciki."
"Muna kwana a fili, wani lokaci ma mukan ji daɗi idan iska ta kaɗa, saboda tana kore sauro.”

- Wata mata

Ta kara da cewa an kwace wayoyinsu, kuma a ko da yaushe 'yan bindigan suna yi musu barazana.

Kara karanta wannan

Bayan jiran kusan shekaru 50, Uba Sani ya kaddamar da hanya a kauyukan Kaduna

“Lokaci mafi muni a gare ni shi ne lokacin da suka yi wa mijina da sauran maza duka. Mun yi kuka tare da tsoron rasa rayukansu, amma ina godiya ga Allah da aka cece mu da rai."

- Wata mata

An yi godiya ga gwamnati da hukumomin tsaro

Wani namiji daga cikin waɗanda suka tsira, wanda shi ma ya nemi a ɓoye sunansa, ya gode wa gwamnatin jihar Kaduna, rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro bisa kokarin da suka yi har aka kuɓutar da su.

"Mun sha wahala sosai a lokacin da muke tsare, amma abin kwantar da hankali shi ne gwamnati ta yi alkawarin kara tsaro, gyaran hanyoyi da sauran ababen more rayuwa a ƙauyenmu.”

- Wani mutum

Haka kuma, an gabatar da saƙonnin fatan alheri daga shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar Kaduna da kuma dattawan ƙauyen Kurmin Wali.

'Yan bindiga sun sako mutanen da suka sace a Kaduna
Gwamna Uba Sani tare da wata yarinya daga cikin wadanda 'yan bindiga suka sako Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Gwamna Uba Sani ya yi jawabi

Jaridar The Nation ta ce da yake jawabi ga waɗanda aka kuɓutar, Gwamna Uba Sani ya bayyana taron a matsayin ranar farin ciki da godiya, yana mai jaddada cewa tsaro shi ne babban abin da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci.

Kara karanta wannan

Harin Kwara ya kara muni, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 80

Da yake ƙarin bayani, gwamnan ya ce jimillar mutane 183 aka sace a lokacin harin. Daga cikinsu, an sako mutane 11 tun da wuri tare da kai su asibiti, 83 sun samu ’yanci kwanaki da suka gabata, yayin da sauran 89 aka kuɓutar da su a ranar Laraba.

'Yan bindiga sun kafa sharuda a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kafa sharuddan da suke so a cika musu kafin su sako masu ibada da suka sace a Kaduna.

'Yan bindigan wadanda suka sace kusan masu ibada 177 sun buƙaci a biya Naira miliyan 250 tare da babura 20 domin sakin su.

Tsagerun yan bindigan sun yi zargin cewa al’ummar Kurmin Wali sun sace babura 17 da aka kwace a hannunsu a lokacin wani samamen sojoji a karamar hukumar Kajuru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng