Dalilin da Ya Sa Aka Nemi Likitoci 'Yan Asalin Kano da ke Aiki a Wasu Jihohi Su Koma Gida
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da daukar likitoci 'yan asalin jihar aiki kai tsaye tare da yi masu tanadi daban-daban
- Gwamnatin Kano ta bukaci duk wani likita 'dan asalin jihar da ke aiki a jihohin makwabta ya dawo gida ya karbi aiki a jiharsa kai tsaye
- A wata sanarwa da shugaban Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ya rattaba wa hannu, ya ce gwamnati ta amince da tsarin albashin likitoci na CONMESS
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ɗaukar likitoci ‘yan asalin jihar aiki kai tsaye, musamman waɗanda a halin yanzu suke aiki a jihohin makwabta.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf na ƙarfafa harkokin kiwon lafiya a asibitocin da ke faɗin jihar.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya bada umarnin daukar likitoci
Daily Trust ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bada umarnin daukar likitocin kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ta hannun Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta bayyana.
Sanarwar ta ce gwamnati na kiran likitocin ‘yan asalin Kano da ke aiki a wasu jihohi da su dawo gida domin karɓar aiki a asibitocin jihar.
Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa ta aiwatar da cikakken tsarin albashin likitoci na CONMESS, kamar yadda gwamnatin tarayya ta tanada.
Bugu da kari, gwamnatin ta ba da tabbacin cewa duk likitan da ya dawo zai ci gaba da aiki matsayin da ya kai a wurin aikinsa na baya.

Kara karanta wannan
Tambuwal ya shiga uku, gwamnatin Sokoto ta taso shi a gaba kan 'badakalar' da N117bn
Tanadin da gwamnatin Kano ta yi wa likitoci
Baya ga albashi, gwamnati ta ce za ta ba likitocin damar cin gajiyar Asusun Horar da Likitocin Ƙwarewa (MRTF), tare da samar da horon cikin gida a wasu fannoni na musamman.
Fannonin da za a horar da likitocin sun haɗa da Cututtukan Jiki, Kiwon Lafiyar Iyali, Cututtukan Kunne, Hanci da Maƙogwaro (ENT), da kuma Kiwon Lafiyar Mata da Haihuwa.
Gwamnatin ta Kano ta ƙara da cewa za a samar da ƙarin alawus da ƙarfafawa nan gaba domin inganta walwala da jin dadin kwararrun likitocin.

Source: Twitter
Gwamnatin ta bukaci dukkan likitocin da suka cancanta, suka cika sharudda da su gaggauta zuwa hedikwatar Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano domin kammala rajista da karɓar aiki nan take.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda, wanda ya ce shirin na da nufin rage gibin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta dakatar da ma'aikatan lafiya
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta tabbatar da batun barin almakashi a cikin maras lafiya, Aishatu Umar a asibitin Abubakar Imam Urology.
Binciken da aka yi cikin gaskiya ya tabbatar da cewa marigayiya Aishatu Umar ta fuskanci matsala bayan wata tiyata da aka yi mata a asibitin.
Hukumar ta ce ta dakatar da ma’aikata uku da aka gano suna da alaka kai tsaye da lamarin daga duk wani mai aikin jinya da asibiti, nan take.
Asali: Legit.ng


