Fadar Shugaban Ƙasa Ta Kashe N34bn a kan Canjin Kuɗi don Tafiye Tafiyen Tinubu
- Rahotanni sun nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe sama da Naira biliyan 34.39 wajen canjin kuɗin waje don tafiye-tafiyen Bola Tinubu
- Kusan Naira biliyan 29.35 daga cikin kuɗin an kashe su ne a shekarar 2024, yayin da shekarar 2025 ta samu raguwar kashe-kashen zuwa Naira biliyan 5.04
- Kudin sun fi karkata ne ga Jiragen Shugaban Ƙasa, abin da ya sake tayar da muhawara kan tsadar tafiyar da jiragen gwamnatin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani binciken ya nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta Najeriya ta kashe aƙalla Naira biliyan 34.39 wajen canjin kuɗin waje domin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje a cikin tsawon shekaru biyu kacal.
Wannan adadi ya fito ne daga bayanan da aka tattara daga GovSpend, wani dandali na bin diddigin kashe-kashen gwamnati da ƙungiyar BudgIT ke tattara wa.

Source: Facebook
Rahoton da ya kebanta ga Punch ya ƙunshi dukkannin mu’amalolin kuɗi da suka shafi Fadar Shugaban Ƙasa da jiragen Shugaban Ƙasa.
Haka kuma ya taɓo Ofishin Shugaban Ma’aikata da kuma ayyukan da suka shafi Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Uwargidan Shugaban Ƙasa, da mataimakansu.
Yadda aka kashe kuɗi kan tafiye-tafiyen Tinubu
Bayanan sun kara da bayyana cewa canji mai girma a tsarin kashe-kashen kuɗin waje ya fi yawa a tsakanin shekarar 2024 da 2025.
Nazarin bayanan ya nuna cewa a shekarar 2024 ne aka fi kashe kuɗin, inda ya kai jimillar Naira biliyan 29.35, yayin da shekarar 2025 ta tsaya ne a kan Naira biliyan 5.04.
Wannan na nufin an samu raguwar kashe-kashen kuɗin waje da kusan kashi 82.8 cikin 100 daga shekarar baya zuwa shekara 2025.

Source: Facebook
Masu nazari sun danganta wannan raguwar da yanayin kasuwar canjin kuɗi, inda aka fara ganin ɗan daidaito a darajar Naira sakamakon sauye-sauyen manufofin gwamnati da kuma ƙarin shigar Daloli daga wasu hanyoyi.
Duk da wannan raguwar, har yanzu yawan kuɗin da ake kashewa kan tafiye-tafiye na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan ƙasa, musamman a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da ƙarancin kuɗin waje da matsin tattalin arziƙi.
Dalilin zuwan Shugaban ƙasa Turkiyya
A baya, kun ji cewa Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya yi karin haske kan dalilin ziyarar da Shugaban Ƙasar Nijeriya ya kai Jamhuriyar Turkiyya.
A cewar Bwala, ziyarar Shugaba Tinubu ba ta zo ne kai-tsaye ba, illa bisa gayyatar da gwamnatin Turkiyya ta yi masa ganin girman Najeriya a nahiyar Afirka da ƙungiyar ECOWAS.
Ya ce wannan gayyata na nuni da girmamawa da martabar da Shugaban Ƙasar ke da ita a idon shugabannin duniya, musamman a fagen diflomasiyya da shugabanci na yankin Afirka ta Yamma.
Asali: Legit.ng

