An ‘Gano’ Wanda Ganduje Ya Yi Zargin Ya Tona Masa Asiri game da Badakala a Kano
- Ana ci gaba da shari'ar da ake zargin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kan badalaka makudan kudi lokacin mulkinsa
- Ganduje ya zargi dan kasuwa da bayyana takardun sirri, amma bincike bai taba bayyana shi a matsayin majiyar bayanai ba
- ’Yan sanda sun kama Ahmad Rabiu a filin jirgin Kano, daga bisani suka gurfanar da shi kan tuhume-tuhume shida na bata suna a gaban kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - sohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi wani fitaccen dan kasuwa kan tona masa asiri.
Gaduje na zargin Ahmad Rabiu, da cewa shi ne ya yada wasu takardun sirri ga jaridu, zargin da aka ce ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
Ganduje ya zargi dan kasuwa kan tuhumarsa
Tsohon gwamnan Kano na zargin dan kasuwar da bankada takardun sirri ga jaridar Premium Times yayin wani bincike da take yi.
Wadannan takardu sun bankado wata badakala ta biliyoyin Naira da ta shafi mallakar Kamfanin tashar sandauri a lokacin mulkin Ganduje a Kano.
Majiyoyi sun rawaito cewa an kama Ahmad Rabiu a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda jami’an ’yan sanda suka cafke shi yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Abuja.
An ce kamen ya biyo bayan wata koke da ’ya’yan Ganduje tare da hadiminsa, Abubakar Bawuro, suka mika wa ’yan sanda.
A cikin koken, sun zargi Rabiu da bai wa jaridar takardun sirri da suka kai ga fallasa zargin cin moriyar mukami da Ganduje ya aikata a lokacin yana gwamna.
Bayan tsare shi na tsawon kwanaki biyu, ’yan sanda suka gurfanar da Ahmad Rabiu a gaban Kotun Tarayya ta Uku a Kano, karkashin Mai Shari’a Samuel Amobede, bisa tuhume-tuhume shida na bata suna.

Source: Facebook
Tuhume-tuhume da ake yi wa Ganduje
Tuhumar ta shafi Ganduje, ’ya’yansa biyu, Umar Abdullahi Umar da Muhammad Abdullahi Umar da kuma hadiminsa Abubakar Sahabo Bawuro. Sai dai Rabiu ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Lauyan kare shi, Maliki Kuliya, ya sanar da kotu cewa sun riga sun shigar da bukatar beli tun ranar 29 ga Janairu, inda ya roki kotu ta saurari bukatar.
Mai gabatar da kara, S. O. Ekwe, ya bukaci dage shari’ar domin ya samu lokaci ya mayar da martani, cewar Punch.
Bayan hutun minti 10, Mai Shari’a Amobede ya amince da bukatar belin, yana mai la’akari da matsayin Maliki Kuliya a matsayin babban lauya kuma tsohon Antoni Janar na Jihar Kano.
Dangane da kamen Rabiu, Muhuyi Magaji, wanda ke gurfanar da Ganduje a babbar kotun jihar Kano, ya ce wannan mataki yunkuri ne na tsoratarwa da lalata shari’ar da ke gudana.
Gwamnatin jihar Kano ta zargi Ganduje da wasu mutane da hada baki wajen canja mallakar kashi 80 cikin 100 na hannun jarin a tashar tsandauri zuwa wani kamfani mai suna City Green Enterprise.
An bayyana cewa Ganduje ya canja hannun jarin gwamnatin Kano na kashi 20 cikin 100 zuwa hannun ’ya’yansa a boye, inda suka zama daraktoci da masu hannun jari, kafin daga bisani a ba kamfanin kwangilar fiye da Naira biliyan 4.
Kano ta gabatar da bukatar cafke Ganduje
A baya, an ji cewa Kotun jihar Kano ta ki amincewa da bukatar kamo tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan zargin karkatar da hannun jarin tashar Dala.
Ana zargin Dr. Ganduje da mallaka wa yayansa guda uku hannun jarin gwamnati da kuma karkatar da Naira biliyan hudu na jama'a.
Wannan shari'a tana ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen shari'a da tsohon gwamnan na Kano yake fuskanta tun bayan barinsa ofis.
Asali: Legit.ng


