Jita Jita Ta Kare: Babban Alkalin Katsina Ya Tsage Gaskiya kan Batun Sakin 'Yan Bindiga 70

Jita Jita Ta Kare: Babban Alkalin Katsina Ya Tsage Gaskiya kan Batun Sakin 'Yan Bindiga 70

  • Ana ta magangantu kan batun shirin gwamnatin jihar Katsina na sakin wasu 'yan bindiga 70 da ke tsare a hannun hukumomi
  • Babban alkalin jihar Katsina, Mai shari'a Musa Abubakar Danladi, ya fito ya yi tsokaci kan lamarin wanda ya jawo cece-kuce
  • Mai shari'a Musa Danladi ya bayyana cewa tun da farko wasu al'ummomi ne suka shiga yin yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga ba tare da sahalewar gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Babban alkalin jihar Katsina, mai shari’a Musa Abubakar Danladi, ya yi magana kan batun sakin 'yan bindiga 70.

Babban alkalin ya karyata rahotannin da ke cewa an sako ‘yan bindiga 70 da ke tsare a jihar, inda ya bayyana ikirarin da kuma martanin jama’a a kai a matsayin marasa tushe.

Babban alkalin Katsina ya ce ba a saki 'yan bindiga ba
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce babban alkalin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata tattaunawa ta musamman a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamna Zulum ya tsage gaskiya kan wanda zai gaje shi a 2027

Ya batun sakin 'yan bindga a Katsina?

Mai Shari’a Musa Abubakar Danladi ya ce babu wani dan bindiga da aka saki, yana mai jaddada cewa rahotannin da ke yawo ba gaskiya ba ne.

Ya sake nanata cewa gwamnatin jihar Katsina ta tsaya tsayin daka kan matsayarta ta kin shiga tattaunawa da ‘yan bindiga, kuma ba ta taba sauya wannan matsayi ba.

A cewarsa, wasu al’ummomin karkara, saboda tsananin hali da suke ciki, sun shiga tattaunawa da ‘yan bindiga da kansu ba tare da izinin gwamnatin jihar ba.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun bukaci a saki mutanen da ke tsare a madadin hakan, lamarin da ya sa al’ummomin suka nemi gwamnati ta shiga tsakani, amma aka ki amincewa.

Me gwamnati ta yi?

Mai shari’a Musa Danladi ya ce maimakon haka, gwamnatin jihar ta nemi shawarwari ta fuskar doka, lamarin da ya kai ga ba da shawarar kafa kwamitin sulhu tsakanin wadanda aka cutar da wadanda suka aikata laifi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun take yarjejeniyar sulhu, sun afkawa Katsinawa

Ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da cewa duk wata mu’amala za ta kasance bisa doka tare da la’akari da hakkin wadanda abin ya shafa.

“Kamar yadda na fada a baya, wasu al’ummomi sun shiga yarjejeniya da ‘yan bindiga ne saboda tsananin halin da suke ciki. Alkalan kotu suna tafiya ne bisa tanadin doka kawai; tausayi ba zai maye gurbin hujja ba."

- Mai shari'a Musa Danladi

An yada cewa gwamnatin Katsina na son sakin 'yan bindiga
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga da dama na tsare

Babban Alkalin ya kara da cewa a lokacin da matsalar ‘yan bindiga ta yi kamari, an kama mutane da dama da ake zargi, inda aka riga aka yanke wa wasu hukunci tare da daure su, yayin da wasu kuma har yanzu ke fuskantar shari’a.

Ya jaddada cewa ba za a iya sakin wadanda aka yanke wa hukunci ba tare da bin ka’idojin doka ba.

“Yanzu haka da nake magana da ku, babu wani dan bindiga da aka sako, dukkansu na fuskantar hanyoyin shari’a ne, don haka hayaniyar da ake yi a kai ba ta da tushe."

- Mai shari'a Musa Abubakar Danladi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Katsina, an kashe jami'an tsaro

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi wa jami'an 'yan sandan kwanton bauna a Katsina.

'Yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin 'yan sanda bayan bude musu wuta a kan hanyar Guga-Bakori a karamar hukumar Bakori.

Hakazalika, 'yan bindigan sun raunata wasu jami'an 'yan sanda biyu inda aka gaggauta garzayawa da su zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng