Bayan Kalaman Akpabio, Ndume Ya Yi Tone Tone kan Dokokin Haraji

Bayan Kalaman Akpabio, Ndume Ya Yi Tone Tone kan Dokokin Haraji

  • Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi tsokaci kan batun yin cushe a sababbin dokokin haraji
  • Ali Ndume ya saba da shugaban majalisar dattawa, wanda ya ce babu wani abu da aka sauya a cikin dokokin wadanda Mai girma Bola Tinubu ya rattabawa hannu
  • Sanatan ya bayyana cewa ko shugaban kwamitin gyaran harajin ya tabbatar da cewa akwai nau'i daban-daban na dokokin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce akwai sabani a cikin dokokin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.

Sanata Ali Ndume ya kara da cewa gwamnatin tarayya na wasa da hankalin ‘yan Najeriya kan lamarin.

Ndume ya yi magana kan dokokin haraji
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Source: Twitter

Ndume ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2027 a shirin Prime Time na tashar Arise TV.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya dauko da zafi, ya tona asirin wasu hadimai na kusa da Shugaba Tinubu

Sanatan ya yi magana ne yayin da yake mayar da martani kan ce-ce-kucen da ke tattare da dokokin harajin.

Me Ndume ya ce kan dokokin haraji?

Ya ce Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji, ya amince cewa akwai “bambance-bambance” da kuma “akalla nau’i biyu” na dokar haraji, inda ya jaddada cewa duk wani gyara dole ne majalisar tarayya ta yi shi.

“Ko shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya amince cewa akwai bambance-bambance, akwai nau’i biyu ko akalla nau’i biyu na dokar haraji, kuma idan za a yi wani abu, dole ne majalisar tarayya ta dauki mataki."

- Ali Ndume

Ndume ya saba da Akpabio

Da yake mayar da martani kan ikirarin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, cewa babu wata matsala, Ndume ya ce wannan ra’ayinsa ne kawai.

“Wannan ra’ayinsa ne. Ni kuwa na yi bincike sosai a kai, sannan dan majalisar wakilai ne ya tayar da batun, kuma ba a karyata shi ba."

- Ali Ndume

Ali Ndume ya kara da cewa majalisar wakilai har yanzu na ci gaba da bincike kan lamarin, yana mai jaddada cewa damuwarsa ita ce yadda ake gudanar da mulki cikin sirri.

Kara karanta wannan

Akpabio ya saɓa da kwamitin majalisa, ya kare Tinubu kan zargin cushe a dokokin haraji

“Matsalata ba wai ko akwai sabani ko babu ba ne, abin da nake damuwa da shi shi ne yin abubuwa a boye. Wannan gwamnati ce ta jama’a, domin jama’a, kuma daga jama’a."

- Sanata Ali Ndume

Ya yi kira ga majalisar tarayya

Ya ce ya kamata shugabannin majalisar tarayya su fito fili su magance batun, yana mai cewa ‘yan majalisa na da ‘yancin bayyana ra’ayinsu ba tare da lakaba musu suna na ‘yan tawaye ba.

“Na kira shugabanni na ce, ‘duba, akwai matsala a nan, domin abin da muka amince da shi ba shi ne abin da shugaban kasa ya sanya wa hannu ba’."

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya ce akwai bambanci a dokokin haraji
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawa Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Source: Facebook

Ndume ya yi gargadi

Ndume ya yi gargadin cewa bai kamata a yi watsi da bambance-bambancen ba, domin dokoki ba sa tsayuwa a kan “tushe mai rikici ba”, inda hakan ka iya jawo kalubale a kotu.

“Ba abu ba ne da za a birne shi kawai, domin yadda ake tafiyar da shi cike yake da sabani da ce-ce-ku-ce."

- Sanata Ali Ndume

Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa an fara aiwatar da dokokin gyaran harajin, yana mai cewa aiwatarwa ba zai yiwu ba matukar akwai nau’o’in dokar da dama a hannun jama’a.

Kara karanta wannan

Sanata ya sake taso da batun harin Amurka a Najeriya, ya fadi kuskuren Tinubu

“Kamar yadda na fada maka, akwai nau’o’i daban-daban a waje, to wanne ne za su aiwatar?”

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya soki hadiman Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya soki wasu daga cikin hadimai na kusa da Shugaba Bola Tinubu.

Ndume ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu yana samun shawarwari marasa kyau daga masu ba shi shawara wadanda ba su fahimci siyasa ko sanin halin da talakawa ke ciki ba.

Sanata Ndume ya ayyana wasu daga cikin hadimin shugaban kasar na yanzu a matsayin wadanda ke rayuwar jin dadi kuma ba su san halin da kasa ke ciki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng