Sojoji Sun Bankado Masana'antar Kera Bindigogi, an Cafke Makeri
- Dakarun rundunar OPWS sun gano wata masana’antar kera bindigogi ba bisa ka’ida ba a Doma, jihar Nasarawa, yayin sintiri na yau da kullum
- An kama wani matashi mai shekaru 26 tare da bindigogin gida da kayan aiki da ake zargin ana amfani da su wajen kera makamai a gidan
- Rundunar ta ce bincike ya zurfafa domin kamo sauran da suka tsere, tare da kiran jama’a da su ba da sahihan bayanai ga hukumomi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa – Dakarun sashen rundunar hadin gwiwa ta Operation Whirl Stroke (OPWS) sun gano wata masana’antar kera makamai ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.
An gano wurin ne yayin wani sintiri na yau da kullum da dakarun da ke sansanin Forward Operating Base, Idadu, ke yi, a wani bangare na kokarin dakile ayyukan ta’addanci da laifuffuka a yankin.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Source: Facebook
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa hoton wanda aka kama a gidan da wasu abubuwan da aka samu a tattare da shi a shafinta na X.
Mukaddashin jami’in yada labarai na OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa an dauki matakan gaggawa bayan gano wurin.
Yadda aka gano wajen kera makamai
Laftanar Ahmad Zubairu ya ce dakarun sun gamu da wasu mutane a wurin da ake zargin masana’antar ke aiki, inda suka tsere suna hango sojoji. Sai dai, an samu nasarar cafke mutum daya yayin da yake kokarin buya a saman bishiya.
Wanda aka kama, Baba Ogar mai shekaru 26, dan kauyen Arusu ne da ke karamar hukumar Kokona, kamar yadda bayanan farko suka nuna.
Bayan cafke wanda ake zargi, dakarun sun fara gudanar da cikakken bincike a wurin, inda aka gano alamun cewa ana kera makamai a wajen tsawon lokaci.

Source: Facebook
Makaman da sojoji suka kwato
A cewar sanarwar, binciken ya kai ga kwato bindigogi guda shida da aka kera, tare da wasu kayayyaki da kayan aiki da ake zargin ana amfani da su wajen kera makamai ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma, an kwato kudi N40,500 da kuma wayar salula da ke hannun wanda aka kama. Rundunar ta ce wadannan kayayyaki na daga cikin muhimman shaidu da za su taimaka wajen binciken da ake yi.
Binciken farko ya nuna cewa wurin yana aiki ne a matsayin cibiyar kera makamai da ake rabawa wasu masu aikata laifuffuka a yankin da ma wasu wurare.
An kashe 'yan bindiga a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta sanar da cewa ta fafata da wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
A cewar rahotanni, an gwabza fada da 'yan ta'addan ne a wasu kauyuka da ke yankin Pindiga a karamar hukumar Akko da ke Gombe.
Jami'an tsaro sun sanar da cewa sun kashe wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen yayin da suka yi musayar wuta da su a cikin daji.
Asali: Legit.ng
