Yadda Jama'a ke Raina Sarki Mai Shekara 22 a Najeriya da Gargadin da Ya Yi
- Fadar Sarki Arujale-Ojime da ke Okeluse a Jihar Ondo ta fitar da sanarwa mai tsauri ga jama’a kan yadda ake kiran sarkin masarautar
- An ce wasu mutane na amfani da kalmomin da ba su dace ba wajen kiran sarkin mai shekaru 22, abin da fadar ta bayyana a matsayin raini
- Fadar ta ce dole ne a rika kiran sarkin da cikakken matsayinsa na sarauta, tare da barazanar daukar mataki kan duk wanda ya saba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo – Fadar Arujale-Ojime na masarautar Okeluse a Jihar Ondo ta gargadi al’umma da su guji kiran sarkin masarautar, Oba Oloyede Adekoya Akinghare II, da kalmomin da ba su dace ba.
Sanarwar ta fito ne a daidai lokacin da ake ta yada labaran cewa wasu mutane na daukar kananan shekarun sarkin a matsayin uzuri na nuna rashin girmamawa gare shi.

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Source: Instagram
Legit ta tattaro bayanai game da sanarwar ne a wani sako da hadimin sarkin, Yarima Adefemi Olorunfemi ya wallafa a Instagram.
Fadar ta bayyana cewa duk da cewa sarkin na daga cikin sarakunan da suka fi kowa karancin shekaru a kasar Yarbawa, hakan ba ya rage masa martabar da ya dace da sarauta.
Gargadin fada kan raina Sarki
Yarima Adefemi Olorunfemi ya jaddada cewa dole ne a rika kiran Oba Oloyede Adekoya Akinghare II da “Mai Martaba Sarkinmu” a kowane lokaci.
Yarima Olorunfemi ya ce wasu mutane na fakewa da kusanci ko sanayya wajen kiran sarkin da kalmomin da ba su dace ba, alhali manufarsu ita ce raina sarauta.
Sanarwar ta ce ba za a lamunci duk wata mu'amala da ba ta dace da matsayin sarkin ba, kuma za a dauki mataki mai tsauri kan duk wanda ya ci gaba da hakan.
Kiran sarki mai shekara 22 ga jama'a
Fadar ta bukaci mazauna masarautar Okeluse da sauran jama’a a ciki da wajen masarautar da su kiyaye mutuncin fada da kuma mutuncin sarkin.
Rahoton TVC ya nuna cewa ta ce girmama sarki ba abu da za a dagawa kowa kafa a kansa ba, kuma komai matsayin mutum, shekarunsa ko matsayinsa a cikin al’umma.
Fadar ta jaddada cewa mutunta sarauta na taimakawa wajen kare al’adu, tarihi da martabar al’ummar Yarbawa gaba daya.

Source: Instagram
Tarihin sarki mai shekara 22
Oba Oloyede Adekoya Akinghare II ya hau gadon sarauta ne yana da shekaru 16 a duniya, a lokacin da yake dalibin makarantar sakandare, bayan rasuwar mahaifinsa wanda shi ne sarkin da ya gabata.
A bisa al’adar garin Okeluse, kasancewarsa tilo namiji a cikin ‘ya’yan marigayin sarki ya ba shi damar gadon sarautar kai tsaye.
Masu zaben sarki sun sanar da shi a matsayin sabon sarkin masarautar, yayin da gwamnatin jihar ta amince da zabin da al’ummar garin suka yi.
Sarkin Badagry ya rasu a Legas
A wani labarin, mun kawo muku cewa Allah ya karbi ran mai martaba Sarkin Badagry, Aholu Menu Toyi I bayan fama da jinya.
Shugaban karamar hukumar Badagry, Babatunde Hunpe ne ya sanar da rasuwar Sarkin, inda ya ce jihar Legas ta yi babban rashi.
Hon. Hunpe ya sanar da cewa bayan samun izinin gwamna Babajide Sanwo-Olu, za a shafe kwana bakwai ana zaman makoki.
Asali: Legit.ng

