Majalisar Dattawa Ta Tabo Batun Kisan Matar Aure da 'Ya'yanta a Kano
- Majalisar dattawa ta yi tsokaci kan kisan gillar da wasu matasa suka yi wa wata matar aure tare da 'ya'yanta shida a jihar Kano
- Shugaban kwamitin 'yan sanda na majalisar dattawa, Ahmad Malam-Madori ya ce lamarin yana matukar tayar da hankali
- Ahmad Malam-Madori ya kuma yabawa rundunar 'yan sandan Najeriya kan yadda suka yi gaggawar cafke wadanda ake zargi da kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi magana kan kisan da aka yi wa wata matar aure da 'ya'yanta shida a Kano.
Majalisar dattawan ta yaba wa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa gaggawar kama mutanen da ake zargi da kashe matar tare da 'ya'yanta.

Source: Facebook
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan Sanda, Sanata Ahmad Malam-Madori ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rattabawa hannu da kansa a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun, 2026.
Sanata Ahmad Malam-Madori ya jinjinawa ‘yan sanda bisa saurin daukar mataki, inda ya ce hakan alama ce ta rundunar da ke kara azama wajen amsa kiran gaggawa.
'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi
Idan za a iya tunawa cewa wani mutum mai suna Umar Auwalu tare da wasu abokan aikinsa biyu sun kashe wata matar aure, Fatima Abubakar, tare da 'ya'yanta shida a unguwar Chiranchi, Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
Rundunar ‘yan sanda, a yayin wani aiki na musamman, ta kama Umar Auwalu da sauran mutum biyu da ake zargi da kisan, awanni 20 kacal bayan aikata wannan mummunan laifi.
Majalisa ta yabawa 'yan sanda
Sanata Madori ya ce saurin da aka yi wajen gano inda waɗanda ake zargi suke tare da cafke su, ya nuna irin karfin aiki da rundunar ‘yan sanda ke kara samu, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Shugaban kwamitin ‘yan sandan, wanda ya bayyana bakin cikinsa matuka kan kisan, ya ce rasa uwa tare da ’ya’ya shida abu ne mai matukar tayar da hankali da taba zuciya.
Ya jaddada cewa, duk da cewa kama mutanen ba zai iya dawo da rayukan da aka rasa ba, gaggawar martanin da ‘yan sanda suka yi, ya nuna cewa ba za a bar laifuffukan tashin hankali su wuce haka kawai ba, kuma za a hukunta masu aikata su bisa doka.
Sanata Ahmad Malam-Madori ya kuma bayyana cewa amfani da tsaron da ke dogaro da bayanan sirri, da kuma tura jami’ai cikin gaggawa, duk suna nuna kyakkyawar hadin kai da ingantaccen tsari a cikin rundunar ‘yan sanda.
Majalisar dattawa za ta goyi bayan 'yan sanda
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa majalisar dattawa za ta ci gaba da goyon bayan gyare-gyaren da ke fifita kwarewa, ɗaukar alhaki da walwalar jami’an ‘yan sanda.
“Rundunar ‘yan sanda mai kwarin gwiwa da kayan aiki na da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a.”
"Dole ne mu rika ba ‘yan sanda isassun kudade. Ba za ka bukaci inganci, sauri da kwarewa daga ‘yan sanda ba alhali ba ka ba su kudin da ya dace ba."
“Tsaro yana bukatar kudade, kayan aiki da mutane. Idan kudade sun yi kadan, bincike zai lalace. Idan aka inganta samar da kudade, saurin daukar mataki zai karu, bayanan sirri su inganta, kuma za a fi kamo masu laifi.”

Kara karanta wannan
Sheikh Daurawa ya je ta'aziyya ga magaidancin da aka kashewa iyali a Kano ya yi masa nasiha
- Ahmad Malam-Madori

Source: Twitter
'Yan sanda na bukatar karin kudade
Ya ce samar da kudade yadda ya kamata na nufin samar da motoci, na’urorin sadarwa, kayan binciken kimiyya da horaswa akai-akai, tare da kula da jin dadin maza da mata da ke sadaukar da rayukansu a kullum.
Sanata Ahmad Malam-Madori ya kuma yaba wa al’ummar Kano da suka bayar da bayanan da suka taimaka wajen nasarar binciken, inda ya jaddada cewa hadin kan jama’a yana da matukar muhimmanci wajen inganta aikin ‘yan sanda.
Ya bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kuma goyon bayan dukkan matakan tsaro na doka.
Daurawa ya je ta'azyyar kisan matar aure
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya je ta'aziyya ga magidancin da aka kashewa matarsa da 'ya'yansa a Kano.
Sheikh Daurawa ya bayyana cewa mummunan lamarin ya tayar da hankalin al'umma a ciki da wajen jihar Kano.
Shugaban na hukumar Hisbah ta Kano ya jajantawa magidancin tare da kwadaitar da shi ya dauki hakuri da juriya kan jarabawar da ta same shi.
Asali: Legit.ng


