Kotu Ta Bayar da Beli ga Kwamishinan Kudi na Bauchi, Ta Gindaya Sharudda Masu Zafi

Kotu Ta Bayar da Beli ga Kwamishinan Kudi na Bauchi, Ta Gindaya Sharudda Masu Zafi

  • Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, da wasu mutum uku sun san matsayarsu kan bukatar neman belin da suka yi
  • Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bukatar da mutanen suka nema ta samun beli a karar da hukumar EFCC ta shigar kansu
  • Mai shari'a Mohammed Umar ya gindaya musu sharudda yayin da ya amince da bayar da belin na su a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Mohammed Umar, ya yanke hukunci kan bukatar neman beli da kwamishinan kudi na Bauchi da wasu mutum uku suka shigar.

Alkalin kotun ya amince da bayar da belin Naira miliyan 100 kowanne ga Yakubu Adamu, tare da sauran waɗanda ake tuhuma da shi, bisa zargin samar da kuɗaɗen ta’addanci har dala miliyan 9.7.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

Kotu ta ba da belin kwamishinan kudi na Bauchi
Kwamishinan kudi na Bauchi na shirin shiga kotu Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Kotu ta bayar da belin Yakubu Adamu

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa alkalin kotun ya yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026.

A cikin hukuncinsa, Mai shari’a Mohammed Umar ya ce Yakubu Adamu da sauran waɗanda ake tuhuma sun gabatar wa kotu da isassun hujjoji da suka ba ta damar amfani da ikon ta cikin adalci da hikima domin amincewa da bukatar belinsu.

Wadanne sharudda kotu ta gindaya?

Alkalin, wanda ya amince da bukatar bayar da belin, ya umarci kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma ya kawo mutane biyu da za su tsaya musu, inda dole ne su kasance babban sakatare da kuma darakta a cikin aikin gwamnati.

Har ila yau, kotun ta umarce su da su ajiye fasfofinsu a ofishin rajistaran kotu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da hakan.

Mai shari’a Mohammed Umar ya kuma bayar da umarni cewa Yakubu Adamu da sauran mutum ukun su kasance suna kai kansu a ofishin hukumar DSS na jihar Bauchi duk ranar Litinin, har sai an kammala shari’ar.

Kara karanta wannan

An yanke wa wani dan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

Daga bisani, alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa 26 ga Fabrairu, domin fara sauraron shaidu.

Tuhume-tuhumen EFCC kan Yakubu Adamu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da tuhuma guda 10 kan zargin samar da kuɗaɗen ta’addanci da wanke kuɗi a kan Yakubu Adamu da wasu mutum uku.

Sauran waɗanda ake tuhuma sun hada da Balarabe Ilelah, Aminu Bose da Kabiru Mohammed, waɗanda aka bayyana a matsayin manyan ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi.

Kotu ta ba da belin Yakubu Adamu
Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu Hoto: Muhammad Audu Sharinah
Source: Facebook

Tun da farko, an hana su beli a gaban Mai shari’a Emeka Nwite, wanda ya kasance alkalin kotu a lokacin hutu a watan Disamban 2025.

Sai dai daga baya an sake gurfanar da su a gaban Mai shari’a Mohammed Umar a ranar 16 ga Janairu, bayan an mika shari’ar ga sabon alkalin.

Bayan sun musanta laifin da ake tuhumarsu da shi, Mai Shari’a Umar ya dage shari’ar zuwa 21 ga Janairu domin yanke hukunci kan bukatar belinsu, wanda daga bisani ya amince da shi.

Kotu ta yi hukunci a shari'ar dan Sule Lamido

Kara karanta wannan

Shari'ar badakalar N1.35bn: Sule Lamido da 'ya'yansa sun san makomarsu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kotun Koli ta yanke hukunci a shari'ar da ke gabanta ta dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Kotun ta yi watsi da karar da Aminu Sule Lamido, ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin da aka yanke masa.

Karar dai ta shafi hukuncin da kotun farko ta yanke, wadda ta same shi da laifin rashin bayyana kuɗaɗen waje har $40,000 a filin jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng