Rikicin Ekid: Gwamna Ya Jawo Wa Kansa, An Nemi Ya Yi Murabus Nan Take

Rikicin Ekid: Gwamna Ya Jawo Wa Kansa, An Nemi Ya Yi Murabus Nan Take

  • Jigon jam'iyyar ADC a jihar Akwa Ibom, Sanata John Akpanudoedehe ya yi kira ga Gwamna Umo Eno ya yi murabus daga kujerarsa
  • Tsohon sanatan ya yi wannan kira ne saboda yadda gwamnan ke nuna karfa-karfa a rikicin da ya barke kam mallakin wani daji a yankin Ekid
  • Rahoto ya nuna cewa mazauna yankin sun yi zanga-zanga ranar Litinin, inda suka nuna adawa da yunkurin gwamnatin jihar Akwa Ibom

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - John Akpanudoedehe, tsohon sanata kuma jigo a jam’iyyar ADC, ya bukaci Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya yi murabus nan take.

Jigon ADC ya yi wannan kira ne biyo bayan zanga-zangar da mutanen Ekid suka yi ranar Litinin kan yadda gwamnan ya kasa magance takaddamar gandun daji na "Stubbs Creek Forest Reserve".

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno a wani taron addu'o'in addinin kirista Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

Abin da ya jawo zanga-zanga a Akwa Ibom

Premium Times ta rahoto cewa al'ummar Ibeno da Ekid sun ce dajin mallakinsu ne yayin da Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ke ikirarin cewa ta riga ta karbe ikon dajin gaba daya.

A baya-bayan nan, ‘yan sanda suka kama tare da gurfanar da wata gimbiya daga masarautar Ekid, God’sown Monday Udoito, bisa umarnin Gwamna Eno.

Sun zarge ta da bata wa Umo Eno suna dangane da rikicin dajin, saboda ta zargi gwamnan da sayar da sassan dajin ga kamfanoni da karkatar da kudaden. A halin yanzu, kotu ta tura ta gidan yarin Uyo.

An nemi Gwamna Eno ya yi murabus

Da yake magana kan tsauraran matakan da gwamnan ya dauka kan lamarin, Akpanudoedehe, tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa, ya ce:

“Dole ne gwamna ya girmama mutanen Ekid ta hanyar yin shawarwari da su, ba wai tsoratarwa da kama mutane don kawai suna kare abin da yake na su ba.

Kara karanta wannan

Tazarce: Gwamna ya jero dalilan da za su sanya ƴan Kaduna su zabi Tinubu a 2027

“Idan har ba ka kama diyarka ba wadda ta zarge ka da kashe mahaifiyarsu, me zai sa ka kama macen da take kare filayen magabata? Ina ganin ya kamata gwamna ya yi murabus idan ba zai iya jure sukar adawa ba."

Tsohon sanatan ya ce a matsayinsa na jagoran adawa a Akwa Ibom, yana da alhakin yin magana duk lokacin da gwamnati ta dauki hanyar da ba ta dace ba.

Zanga zanga.
Matasan da suka fito zanga-zanga kan dajin Ekid da ake zargin Gwamna Umo Eno ya karbe a Akwa Ibom Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

An bukaci Gwamna Eno ya saki Udoito

Ya bukaci gwamnan da ya janye tuhume-tuhumen da ake yi wa Princess Udoito kuma ya ba da umarnin sako ta nan take, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu, Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ba ta mayar da martani kan kiran na murabus ba.

A ranar Litinin, wasu matasa a Eket su kan yi biris da gargadin ‘yan sanda inda suka fito zanga-zanga kan yadda Gwamna Eno ke tafiyar da rikicin dajin Stubbs Creek.

Mata sun gargadi gwamnan Akwa Ibom

A wani labarin, kun ji cewa tashin hankali ya ci gaba da mamaye al’ummar yankin Ekid a jihar Akwa Ibom, biyo bayan kama Princess God’sown Udoito.

Kungiyar mata ta Ekid Women Wing, wacce ta kunshi mata daga Eket da Esit Eket, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira danniya karkashin mulkin Gwamna Umo Eno.

Matan sun ce sun yanke shawarar kaurace wa dukkan harkokin siyasa har sai an saki Princess Udoito daga gidan yari ba tare da wani sharadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262