Bayan Kisan Kano, Miji Ya Kashe Matarsa da Fartanya a Kebbi
- Rundunar ’yan sandan Kebbi ta cafke Sule Gurmu bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a wani rikicin cikin gida da ya tayar da hankula a karamar hukumar Augie
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 13, Janairu, 2026, inda ake zargin mutumin ya buge matar tasa da kotar fartanya, abin da ya kai ga rasuwarta
- Bayan tserewa zuwa wata jiha, jami’an tsaro sun gano inda yake tare da cafke shi, lamarin da ya sake jaddada bukatar daukar matakai kan rikici tsakanin ma'aurata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kebbi – Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta sanar da cafke wani mutum mai suna Sule Gurmu, wanda ake zargi da kashe matarsa, Umaima Maidawa, mai shekaru 25, a Bayawa da ke karamar hukumar Augie.
A cewar ’yan sanda, lamarin ya faru ne a ranar 13, Janairu, 2026, yayin da rikici ya barke tsakanin ma’auratan a gidansu. Ana zargin Gurmu ya yi amfani da fartanya wajen dukan matarsa, wannan ya jawo mutuwarta.

Source: Original
Rundunar 'yan sandan jihar ta wallafa a Facebook cewa bayan faruwar lamarin, hukumomin tsaro suka fara bincike duk da wanda ake zargi ya tsere.
Miji ya kashe matarsa da fartanya
Bayanan ’yan sanda sun nuna cewa rigimar cikin gida ce ta janyo tashin hankalin da ya kai ga kisan. Jim kadan bayan bugun da aka yi wa Umaima da fartanya, an tabbatar da mutuwarta.
Shugaban karamar hukumar Augie, Yahaya Augie, ya kai ziyara wajen da abin ya faru domin ganin halin da ake ciki. Ya kuma taimaka wajen daukar gawar marigayiyar zuwa Asibitin Argungu domin yin bincike.
An kama mijin da ya kashe matarsa
Punch ta rahoto cewa bayan tserewarsa, 'yan sanda sun fara farautar Sule Gurmu a tsakanin yankunan jihohin Kebbi da Sokoto.
Rundunar ’yan sanda tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaro ta NSCDC suka gudanar da aikin bin diddigi, har suka cafke shi a garin Katami da ke karamar hukumar Silame a Sokoto.
An ce cafke shi ya biyo bayan umarnin da shugaban karamar hukumar Augie ya bayar, inda ya bukaci a kamo wanda ake zargi ba tare da bata lokaci ba.

Source: Facebook
Shugaban karamar hukumar ya yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka gudanar da aikin cikin kwarewa, yana mai jaddada cewa ba za a lamunci aikata laifi ko tashin hankalin cikin gida a yankin ba.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da cafke Gurmu, yana mai cewa za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike.
An kashe mata da 'ya'yanta 6 a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da kashe wata mata da 'ya'yanta har guda shida a wata unguwa a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun 'yan sanda sun yi nasarar kama mutum uku da ake zargi suna da hannu a kashe mutanen da aka yi.
Biyo bayan tambayoyi da aka yi wa wadanda aka kama, daya daga cikinsu ya amsa cewa yana da hannu a lamarin kuma ba wannan ne karon farko da suka yi kisa ba.
Asali: Legit.ng

