CAN Ta Yi Jimamin Rasuwar Malamin Musuluncin da Ya Ceci Kiristoci a Rikicin Plateau

CAN Ta Yi Jimamin Rasuwar Malamin Musuluncin da Ya Ceci Kiristoci a Rikicin Plateau

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta yi alhinin rasuwar Malam Abubakar Abdullahi wanda ya rasu yana da shekara 90
  • Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya nuna jarumta ta musamman saboda kare rayukan Kiristocin da ya yi
  • Kungiyar CAN ta mika ta'aziyya ga iyalan marigayin wanda ta bayyana a matsayin mutumin da ya mutunta ran dan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta jajanta wa iyalan Mallam Abubakar Abdullahi, wani limami a jihar Plateau.

Mallam Abubakar Abdullahi ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 90 a duniya bayan fama da rashin lafiya.

CAN ya yi jimamin rasuwar Malam Abubakar Abdullahi
Malamin addinin Musulunci, marigayi Mallam Abubakar Abdullahi Hoto: blackexcellence
Source: Instagram

Jaridar Vanguard ta ce shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta’aziyya da ya fitar a ranar Asabar, 17 ga watan Janairun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya turo sako daga kasar waje kan rasuwar malamin Musulunci a Najeriya

CAN ta kadu kan rasuwar Malam Abubakar

Shugaban na CAN ya bayyana marigayin a matsayin “abin koyi" wajen zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Marigayin malamin ya shahara bayan da ya ceto rayukan Kiristoci 262 a gidansa da masallacinsa a lokacin wani rikici a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.

Okoh ya ce tarihin da limamin ya bari zai ci gaba da kasancewa sakamakon “jarumta ta musamman” da ya nuna, musamman a lokacin kisan kiyashin da ya faru a Plateau a shekarar 2018.

“Ta hanyar yanke shawarar kare rayukan bayin Allah marasa laifi duk da haɗarin da ke tattare da hakan, ya tsaya tsayin daka don kare rayuka a lokacin da ya fi dacewa."
"Ayyukansa sun wuce iyakokin addini, kuma sun tabbatar da cewa mutuncin rayuwar ɗan Adam abu ne mai muhimmanci fiye da komai."

- Daniel Okoh

CAN ta tuna da jarumtakarsa

Shugaban CAN ya lura da cewa jarumtar limamin ta zama tarihi na haɗin kai a kasa da ke yawan fuskantar shakku tsakanin addinai.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci 260 a rikicin Plateau ya rasu

“Ayyukansa sun tunatar da kasa cewa zaman lafiya na yiwuwa ta hanyar kauna da mutunta juna."
“Ya wakilci muhimman abubuwan imani, tausayi da sadaukar da kai. Ko da yake kyaututtukan zahiri na iya shuɗewa, labarinsa ya kasance abin koyi ga al’ummomi masu zuwa."

- Daniel Okoh

CAN ta yi jimamin rasuwar Malam Abubakar Abdullahi
Marigayi Malam Abubakar Abdullahi wanda ya ceci Kiristoci a Plateau Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban CAN ya ba gwamnati shawara

Ya kuma yi kira ga gwamnati da jama’a da su tabbatar cewa sadaukarwar limamin ta zama abin haɗa kai wajen gina Najeriya mai zaman lafiya.

“Yayin da muke jimamin rasuwarsa, muna kuma murnar rayuwar da ya yi ta alheri. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, al’ummarsa da duk waɗanda misalinsa na ban mamaki ya taɓa."

- Daniel Okoh

A baya gwamnatin tarayya ta ba Mallam Abubakar Abdullahi lambar yabo ta Order of the Niger (OON) domin girmama gudummawarsa wajen bunƙasa zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Malam Abubakar

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ta'aziyyar rasuwar malamin addinin Musulunci a Plateau.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Gwamnatin tarayya ta gamu da cikas a shirin aiwatar da dokar haraji

Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa, inda ya bayyana marigayi limamin a matsayin malami na musamman.

Mai girma Tinubu ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da su yi koyi da rayuwar Imam Abubakar ta hanyar wa’azi, girmama juna da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng