'Yan Sanda Sun Samo Mafita ga 'Yan Najeriya idan Suka Hadu da Masu Neman Rayuwarsu

'Yan Sanda Sun Samo Mafita ga 'Yan Najeriya idan Suka Hadu da Masu Neman Rayuwarsu

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ba da shawara ga 'yan kasa idan suka tsinci kansu a hannun mutanen da ke dauke da makamai da ke neman rayuwarsu
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya ya bayyana cewa a irin wannan yanayi ba yin fada ba ne abin da ya kamata mutane su rika yi
  • Benjamin Hundeyin ya kuma bayyana cewa rundunar 'yan sandan na samun nasarori sosai a yakin da take yi sa masu aikata laifuffuka a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan Najeriya ta shawarci ’yan kasa kan abin da ya kamata su yi idan suka ci karo da masu aikata laifuffuka da ke neman rayuwarsu.

Rundunar 'yan sandan ta shawarce su kada su yi yunkurin tsayawa gardama ko faɗa idan suka tsinci kansu a cikin wani yanayi mai hatsari tare da masu aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

'Yan sanda sun bukaci 'yan Najeriya su fifita kare kansu
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Najeriya, Benjamin Hundeyin, ya bayar da wannan shawara a ranar Talata, 13 ga watan Janairun 2026, yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.

'Yan sanda sun ba 'yan Najeriya shawara

Benjamin Hundeyin ya yi kira ga jama’a da su fifita kare rayukansu fiye da komai saboda hakan shi ne abin da ya fi muhimmanci.

Ya ce ya dace jama’a su kasance cikin natsuwa a irin waɗannan yanayi, yana mai jaddada cewa kare rai ya fi muhimmanci fiye da tunkarar mutanen da ke amfani da makami da tashin hankali wajen aikata laifuffuka.

“Idan aka yi rashin sa’a ka tsinci kanka a hannun masu aikata laifi, kada ka yi gardama, kada ka yi faɗa, ka zauna lafiya kawai ka ceci ranka da farko. A kowane lokaci za mu iya bin waɗannan masu laifi domin a kama su."

- Benjamin Hundeyin

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke mutane 3 dauke da kayayyakin hada bama bamai a Daura

Jami'an 'yan sanda na samun nasarori

Mai magana da yawun ’yan sandan ya kuma bayyana cewa rundunar ta samu ci gaba wajen yaki da kungiyoyin masu aikata laifuffuka, ciki har da fitattun kungiyoyin ’yan fizge da ke aiki a wasu sassan Abuja.

Kakakin 'yan sanda ya ba 'yan Najeriya shawara
Mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya, Benjamin Hundeyin @BenHundeyin
Source: Facebook

A cewarsa, an samu nasarar kama wasu mutane a baya-bayan nan dangane da ayyukan wannan ƙungiya, ciki har da waɗanda ake zargi da hannu a kisan wata lauya a babban birnin tarayya Abuja.

“Har ila yau, mun samu gagarumar nasara wajen kama ’yan wannan kungiyar ta masu fizge. Kwanaki kaɗan da suka wuce, mun kama kungiyar da ke da alhakin kisan wancan lauya, sannan an kwato wayar ta."

- Benjamin Hundeyin

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga dauke da makamai a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya

Rundunar 'yan sandan ta ce jami'anta sun samu nasarar hallaka mutane biyu daga cikin ’yan bindigan are da kwato makamai daga hannunsu.

An samu nasarar aikin ne bayan samu sahihin bayanan sirri kan cewa ’yan bindiga na shirin kai hari kauyen Idisu, da ke gundumar Idisu a yankin Bayan Kogi

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng