Malami: Lauya Ya Fallasa Munafuncin 'Yan Adawa kan Shari'ar Tsohon Ministan Buhari
- Ana ci gaba da muhawara kan gurfanar da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, da hukumar EFCC ta yi a gaban kotu
- Waau 'yan adawa sun caccaki hukumar inda suke zarge ta da farautar mutanen da ba sa cikin gwamnati da jam'iyyu mai mulki
- Sai dai, lauya kuma dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju, ya fito ya yi wa 'yan adawa ta-tas, inda ya zarge su da nuna munafunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama kuma lauya, Deji Adeyanju, ya caccaki jam’iyyun adawa kan abin da ya kira sukar da suke yi wa hukumar EFCC.
Adeyanju ya caccaki 'yan adawa kan yadda suke sukar matakan da hukumar EFCC ta dauka game da tsohon Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana wadannan ra’ayoyi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026.
Me Deji Adeyanju ya ce kan 'yan adawa?
Adeyanju ya bayyana damuwarsa da takaicinsa kan yadda jam’iyyun adawa ke nuna irin wannan halayya, yana mai cewa ya kamata su tsaya kan gaskiya da adalci.
Lauyan ya kuma bukaci su nuna goyon baya ga yaki da cin hanci da rashawa, maimakon kokarin raunana ko zargin hukumomin yaki da rashawa.
Ya jaddada cewa ya dace jam’iyyun adawa su mara wa yaki da cin hanci da rashawa baya ba tare da la’akari da jam’iyya ba.
Lauya ya ba 'yan adawa shawara
A cewarsa, jam’iyyun adawa su ne ya kamata su kasance a sahun gaba wajen neman bin diddigin ayyukan masu rike da mukaman gwamnati, ko suna cikin jam’iyyar mulki ko ta adawa.
“Ina matukar damuwa da abin da nake gani a matsayin munafunci a martanin wasu ‘yan adawa dangane da kama tsohon Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN."
“Ba za ka ce kana son ingantacciyar Najeriya ba, amma kuma kana nuna kamar kana kare mutanen da ake zargi da manyan laifuffukan cin hanci da rashawa. Abin da ake bukata shi ne tsayayyen tsari na neman gaskiya da bin doka.”
- Deji Adeyanju
Me Adeyanju ya ce kan shari'ar Malami?
Adeyanju ya jaddada cewa akwai zarge-zarge da ake yi wa Malami, kuma irin wadannan zarge-zarge ya kamata a bincike su dalla-dalla ta hannun hukumomin da doka ta tanada.
“Abin da jam’iyyun adawa ya kamata su rika nema shi ne bincike na gaskiya ba wai sukar EFCC ko kokarin bata sunan ayyukanta ba."
- Deji Adeyanju
Mai fafutukar ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji kokarin bata sunan EFCC, yana mai cewa a maimakon haka ya dace a karfafa wa hukumar gwiwa ta gudanar da aikinta cikin kwarewa da ‘yanci ba tare da katsalandan ba.

Source: Twitter
Ya kuma yi nuni da yadda EFCC ke tafiyar da wasu manyan shari’o’i, yana mai cewa hakan na daga cikin aikin da aka dora wa hukumar na binciken duk wanda ake zargi da cin hanci da rashawa, tare da jaddada cewa babu wanda ya fi karfin doka.

Kara karanta wannan
Halin da masu zuwa Mauludi suke ciki bayan kwashe kwanaki hannun 'yan bindiga a Plateau
“Idan har Najeriya da gaske take kan yaki da cin hanci da rashawa, dole ne mu daina kare mutane saboda siyasa, mu dage cewa duk wani zargi a bincike shi yadda ya kamata, sannan a gurfanar da wanda ake zargi bisa doka."
- Deji Adeyanju
Kotu ta ba da belin Abubakar Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya samu beli a wajen babbar kotun tarayya Abuja.
Kotun ta ba da belin ne ga Abubakar Malami, dansa Abdul'aziz Malami da matarsa Asabe Bashir bayan ta gindaya musu sharudda masu tsauri.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin bayar da belin ya ce kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma zai bayar da Naira miliyan 500 a matsayin beli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

