An Yi Babban Rashi: Shugaban Jam'iyyar APC da Wasu Manyan 'Yan Siyasa 2 Sun Mutu
- Jam’iyyar APC a jihar Kogi ta girgiza sakamakon rasuwar mambobinta uku da suka hada da masu ba wa gwamna shawara da shugaban mazaba
- Gwamna Ahmed Usman Ododo ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arzikin mamatan tare da yaba wa irin gudunmawar da suka bayar
- Hon. Onojah James Ignatius ya rasu ne a ranar Asabar a birnin Lokoja bayan ya dawo daga ziyarar da ya kai wa mahaifarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Jam’iyyar APC reshen jihar Kogi tana cikin yanayin makoki sakamakon rashin mambobinta guda uku da suka riga mu gidan gaskiya a lokuta daban-daban.
Gwamnatin Kogi ta bayyana wannan rashi a matsayin babban gibi ga jam’iyya da kuma jihar baki ɗaya, tana mai bayyana mamatan a matsayin mutane masu kishin al'umma da sadaukarwa.

Source: Twitter
Shugaban APC da kusoshi 2 sun mutu
Waɗanda suka rasun sun haɗa da Hon. Onojah James Ignatius, tsohon shugaban karamar hukumar Igalamela kuma mashawarci na musamman ga gwamnan jiha, in ji rahoton Tribune.
Sauran sun hada da; Hon. Jatto Onimisi Suleiman, babban mataimaki na musamman ga gwamna; da kuma Alhaji Alih Atabo, shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Anyigba a ƙaramar hukumar Dekina.
Hon. Onojah James Ignatius ya rasu ne a yammacin ranar Asabar a garin Lokoja, jim kaɗan bayan ya dawo daga ƙauyensa.
Gwamnatin Kogi ta bayyana wannan rashi a matsayin babban gibi ga jam’iyya da kuma jihar baki ɗaya, tana mai bayyana mamatan a matsayin mutane masu kishin al'umma da sadaukarwa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar da sanarwa a ranar Lahadi inda ya miƙa ta’aziyyar Gwamna Ahmed Usman Ododo ga iyalai da daukacin mambobin APC.
An tuna da sadaukarwar kusoshin APC
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Waɗannan mutane sun yi wa Jihar Kogi da jam’iyyar APC hidima da sadaukarwa da biyayya mara misaltuwa.
"Hon. Onojah mutum ne mai fafutukar ci gaban karkara kuma gogaggen mai shirya jama'a ne wanda sha'awarsa ga ci gaban al'umma da kyakkyawan shugabanci ya fito fili a dukkan harkokinsa.”
Haka zalika, an bayyana Hon. Jatto Onimisi Suleiman a matsayin jami'i wanda ya gudanar da ayyukansa cikin ƙanƙan da kai, ƙwazo, da kuma matuƙar riƙon amana, inda a koyaushe yake sanya muradin jama'a sama da na kansa.

Source: Facebook
Gwamna ya yi ta'aziyyar mambobin APC
Gwamnatin ta kuma yaba wa Alhaji Alih Atabo, inda ta bayyana shi a matsayin jajirtaccen jagoran jam'iyya wanda ya sadaukar da kansa wajen dorewar haɗin kai da ci gaban APC a matakin mazaɓa.
Gwamna Ododo ya tura saƙon jaje ga mutanen Igalamela, Okene, da Dekina, yana mai jaddada cewa gudunmawar da waɗannan mashahuran mutane suka bayar wajen gina jihar ba za ta taɓa mancewa ba.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa 2 sun fice daga jam'iyyar PDP, sun gana da shugaban gwamnonin Arewa
Sanarwar ta ƙarkare da addu’ar Allah ya jikan mamatan, sannan ya ba wa iyalansu haƙurin jure wannan rashi mai matuƙar raɗaɗi da ba zai taɓa mayu raba ba.
Shugaban jam'iyyar APC ya rasu a Kogi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kogi ta Gabas, Suleiman Omika Mohammed, ya rasu yana da shekara 45.
An ruwaito cewa Omika Mohammed, wanda ya maye gurbin Nasir Agbodu a matsayin shugaban jam'iyyar ƴan watanni da suka gabata, ya rasu cikin yanayin ban al'ajabi.
A cewar ƴan uwansa, marigayin yana hutawa ne a gidansa da ke Lokoja, babban birnin jihar, lokacin da ya fara kururuwar neman agaji yana cewa yana jin karfin jikinsa na raguwa, sai ya faɗi nan take ya rasu.
Asali: Legit.ng

