Bayan Janye Korafinsa a ICPC, Dangote Ya Kai Karar Tsohon Shugaban NMDPRA a EFCC

Bayan Janye Korafinsa a ICPC, Dangote Ya Kai Karar Tsohon Shugaban NMDPRA a EFCC

  • Mashahurin attajiri, Aliko Dangote ya sake mayar da tsohon Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed gaban EFCC
  • A wannan karon ma, korafin da Dangote ya shiga ya zargi Farouk Ahmed da cin hanci da rashawa da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba
  • Dangote ya ce zai gabatar da hujjoji don tabbatar da zarge-zargen da ya ke yi wa tsohon Shugaban wajen jami'an EFCC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban Dangote, Aliko Dangote, ta hannun lauyansa, ya shigar da ƙara a hukumance kan tsohon Babban daraktan hukumar kula da man fetur ta Ƙasa, NMDPRA, Farouk Ahmed, a EFCC.

Wannan na kunshe a ckin wata aka fitar a ranar Juma'a inda aka ce Dangote ya kuma shigar da ƙarar ta EFCC bayan “janye wacce ya kai hukumar ICPC da fari.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Dangote ya kai Farouk Ahmed gaban EFCC
Alhaji Aliko Dangote tare da Farouk Ahmed Hoto: Zainab Nasir Ahmad
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa a baya y ce ya kai ƙara ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) don a binciki Farouk Ahmed kan zargin kashe $5m wajen karatun sakandaren ‘ya’yansa a Switzerland.

Sai dai, ya janye ƙarar kwanaki kadan da suka wuce, duk da cewa ICPC ta ce za ta ci gaba da bincike kamar yadda dokar kasa ta ba ta dama.

Dangote ya kai Farouk Ahmed EFCC

Daily Post ta ruwaito cewa a cikin ƙarar da Babban Lauya Dr. O.J. Onoja ya sa hannu, Dangote ya bukaci EFCC ta gudanar da bincike kan zarge-zargen amfani da mukami ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma yana so a binciki Farouk Ahmed a kan zargin samun dukiya ta hanyar rashawa, sannan a gurfanar da shi idan aka tabbatar da laifinsa

Dangote na zargi Farouk Ahmed da rashawa
Alhaji Aliko Dangote, Shugaban kamfanonin Dangote Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Sanarwar ta ƙara da cewa Dangote zai samar da hujjoji don tabbatar da zarge-zargen da cin hanci da rashawa da aka yi.

Kara karanta wannan

Duk da janye korafin Dangote, ICPC ta taso tsohon shugaban NMDPR a gaba

Onoja ya bukaci hukumar, karkashin jagorancin Mr. Olanipekun Olukoyede, ta binciki ƙorafin cin hanci da rashawa da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da ake yiwa Injiniya Farouk Ahmed.

ICPC na binciken Farouk Ahmed

Duk da fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya janye karar da ya shigar gaban hukumar ICPC da fari, hukumar ta ce za ta ci gaba da aikinta.

Ta bayyana cewa dokar Najeriya ta ba ta dama ta binciki duk wani da ake zargi da yi wa tattalin arzikin kasa da dukiyar jama'a almundahana.

Hukumar ta ce janye korafin da Dangote ya yi ta hannun lauyoyinsa ba zai hana shi ci gaba da aiki a kan zarge-zargen da ke gabanta ba.

Tonon sililin Dangote ya ci kujerar Farouk Ahmed

A baya, mun wallafa cewa attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya tona abin da ya kira badakalar cin hanci da rashawa a wasu manyan hukumomin gwamnati da ke da alaka da ma’aikatar man fetur.

Dangote ya yi ikirarin cewa wasu manyan jami’ai a hukumomin NMDPRA da kuma NUPRC sun shiga harkokin da ba su dace ba, lamarin da ya jawo hankalin jama’a da hukumomin yaki da cin hanci.

Kara karanta wannan

2027: Ana kulla wa EFCC makarkashiya, hukumar ta fallasa shirin ƴan adawa

Zargin da Dangote ya yi ya zama daya daga cikin dalilan da suka haddasa rasa kujerun shugabannin hukumomin biyu, abin da ya kara dagula lamarin a fannin man fetur a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng