'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka cikin Dare, An Yi Awon Gaba da Mutane a Katsina
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina
- Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama a yayin hare-haren da suka kai cikin kauyukan da daddare
- Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun dauki lokacin suna barna tare da sanya jama'a cikin firgici yayin hare-haren da suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - ’Yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hare-hare kan wasu kauyuka a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun sace mutane da dama a jerin hare-haren dare da suka gudana lokaci guda.

Source: Facebook
Shaidun gani da ido sun tabbatar da kai harin ga tashar Channels Tv ta wayar tarho a ranar Talata, 6 ga watan Janairun 2025.
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Katsina
Sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne a daren Litinin, 5 ga watan Janairun 2025 lokacin da ’yan bindigan da ke dauke da manyan makamai suka mamaye yankunan da abin ya shafa.
Tsagerun 'yan bindigan sun kwashe tsawon sa’o’i suna barna da tayar da hankulan jama'a a kauyukan da suka kai hare-haren, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun fara kai hari ne a Unguwar Alhaji Barau, daga nan suka wuce zuwa Gidan Dan Mai-gizo da kuma Gidan Hazo, dukkansu na cikin gundumar Na’alma a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, kuma har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ba.
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya bayya cewa bai samu labarin harin ba, amma ya yi alkawarin bincike tare da bayar da bayani.
“Don Allah bari na bincika, domin yanzu ne kawai nake jin labarin harin daga gare ku. Zan dawo da bayani."
- Abubakar Sadiq

Source: Original
'Yan bindiga na kai hare-hare a Katsina
Malumfashi na daga cikin kananan hukumomin Katsina da ke sahun gaba wajen fuskantar hare-haren ’yan bindiga, duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka shiga kwanan nan tsakanin shugabannin yankin da wasu kungiyoyin masu dauke da makamai.
Sababbin hare-haren sun zo ne bayan harin masallaci da ya faru a ranar 19 ga Agusta, 2025, inda ’yan bindiga suka kai farmaki wani masallaci, suka bude wuta kan masu ibada, suka kashe akalla mutane 32 a Unguwar Mantau, karamar hukumar Malumfashi.
Jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasara bayan sun gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Jami'an tsaron sun samu nasarar ceto mutane 20 da 'yan bindigan suka sace daga kauyen Dunfawa da ke yankin Moriki, a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Aikin ceto mutanen ya samu nasara ne bayan hadin kai da tsare-tsaren jami’an tsaro da aka tura yankin, wanda ya tilasta wa ‘yan bindigan barin wadanda suka sace sannan suka tsere.
Asali: Legit.ng

