Jirgi Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Haɗari a Najeriya, Mutum 25 Sun Mutu, 14 Sun Ɓace
- Rahoto ya nuna cewa akalla mutum 25 ne suka rasu yayin da wasu 14 suka bace bayan wani jirgin ruwa ya kife a garin Nguru
- Hukumar SEMA ta tabbatar da cewa mutane goma 13 aka ceto da rai, sannan jami'an agaji na ci gaba da neman sauran mutum 14
- Hatsarin ya faru ne lokacin da jirgin dake dauke da fasinjoji hamsin da biyu yake dawowa daga jihar Jigawa zuwa jihar Yobe daddare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Aƙalla mutane 25 ne ake fargabar sun rasa rayukansu, yayin da wasu 14 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a ƙaramar hukumar Nguru da ke jihar Yobe.
Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:48 na daren ranar Asabar, lokacin da jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 52 yake kan hanyarsa ta dawowa daga garin Adiyani na jihar Jigawa zuwa garin Garbi da ke jihar Yobe.

Source: UGC
Jirgin ruwa ya kife da mutane a Yobe
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa akasarin fasinjojin manoma ne da masunta waɗanda suka tafi kasuwanci da sauran ayyukan yau da kullum.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin babban sakatarenta, Mohammed Goje.
Ya bayyana cewa bayan samun kiran gaggawa, hukumar ta tura jami'anta daga ƙananan hukumomin Bade da Nguru domin haɗa kai da jami'an tsaro da dakarun sa-kai na yankin wajen gudanar da aikin ceto.
Zuwa yanzu, Mohammed Goje ya ce an yi nasarar ceto mutum 13 da ransu, waɗanda aka garzaya da su asibiti domin karɓar magani.
Fasinjoji 14 sun ɓace a cikin ruwa
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da gagarumin aikin bincike a cikin ruwan domin gano ragowar mutane 14 da har yanzu ba a san inda suke ba, in ji rahoton The Cable.
Goje ya tabbatar da cewa gwamnati tana yin duk abin da za ta iya domin ganin an gano kowa, sannan an bai wa waɗanda aka ceto cikakken tallafi na jinkai da na lafiya.
Wannan haɗari ya sake tayar da damuwa kan tsaron sufurin ruwa a yankunan karkara, musamman a lokutan da ruwa ke cika ko kuma lokacin tafiye-tafiyen dare.

Source: Original
An koka kan yawaitar hadurran jiragen ruwa
Wannan mummunan lamari ya jefa al'ummomin jihohin Jigawa da Yobe cikin baƙin ciki, inda iyalai ke jiran labarin masoyansu.
Masu sa ido sun yi kira ga hukumomi da su samar da ingantattun rigunan kariya da kuma tsaurara dokoki kan yawan fasinjojin da jiragen ruwa ya kamata su ɗauka.
Ana sa ran samun ƙarin bayani daga hukumar SEMA yayin da aikin ceto ke ci gaba da gudana a cikin kwanaki masu zuwa.
Jirgin ruwa ya kife da mutane a Legas
A wani labari, mun ruwaito cewa, fasinjoji shida sun mutu yayin da aka ceto mutane hudu bayan wani jirgin ruwa ya yi hatsari a tsakiyar tekun Legas.
Hukumomin LASWA da NIWA sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon karon da jirgin ya yi da wani abu a cikin ruwa.
Jami'an aikin ceto na ci gaba da yin nutso cikin ruwa don tabbatar da cewa babu wani fasinja da ya rage a karkashin ruwa bayan hatsarin.
Asali: Legit.ng

