"Ba Tinubu ba ne": Sanata Ya Fadi Masu Alhakin Samar da Tsaro

"Ba Tinubu ba ne": Sanata Ya Fadi Masu Alhakin Samar da Tsaro

  • Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kamata a rika dorawa alhaki ba kan matsalar rashin tsaro a jihohi
  • Tsohon gwamna nuna cewa lokacin da yake mulkin Abia a matsayin Gwamna, ta kasance jiha mafi tsaro a kaf din tarayyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ebonyi - Sanata Orji Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Sanata Kalu ya ce ‘yan Najeriya su daina ɗora laifin matsalar tsaro kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Kalu ya ce gwamnoni ke da alhakin samar da tsaro a jihohinsu
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa Sanata Kalu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Janairun 2026 a Ekoli Edda, karamar hukumar Edda ta jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

'Shugaba Bola Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna'

Ya yi maganar ne yayin wata ziyara ta sabuwar shekara da ya kai wa Stanley Emegha, shugaban jam’iyyar APC a jihar Ebonyi.

Sanata Kalu ya ba gwamnonin jihohi shawara

Sanatan ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su ɗauki cikakken alhakin tsaron jihohinsu, yana mai cewa ba za a magance matsalar rashin tsaro ba sai gwamnonin sun dauki ragamar batun tsaro a yankunansu.

"Ba za a iya shawo kan matsalar tsaro ba sai gwamnonin jihohi sun ɗauki nauyin tsaro a hannunsu.”

Sanata Kalu ya yaba wa Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi, yana mai cewa ya nuna kwarewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar, jaridar The Nation ta kawo labarin.

Haka kuma, ya ce jihar Abia ita ce mafi tsaro a Najeriya a lokacin da yake gwamna.

"A lokacin da nake gwamnan jihar Abia, ita ce mafi tsaro a duk Najeriya. Lokacin da nake gwamna, jihohi da dama sun rushe ta fuskar tsaro, har da Warri da Port Harcourt. Amma Aba ta kasance lafiya, domin babu satar mutane a jihar Abia.”

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya sha alwashin korar gwamna daga mulki, zai iya yin komai a 2027

- Sanata Orji Uzor Kalu

Kalu ya wanke Tinubu kan rashin tsaro

Ya kara da cewa bai dace a ci gaba da zargin shugaban kasa kan matsalar tsaro ba.

“Wasu na cewa Shugaba Tinubu ya yi wannan ko wancan don kawo karshen rashin tsaro, a’a. Lokacin da nake gwamna, na ɗauki alhakin tsaron Abia, kuma babu wanda zai motsa ba tare da an kare rayuka da dukiyar jama’a ba.”

- Sanata Orji Uzor Kalu

Sanatan ya bukaci sauran gwamnonin jihohi da su kwaikwayi tsarin tsaron da ake aiwatarwa a jihar Ebonyi.

“Ya kamata gwamnonin su koma su kare jihohinsu kamar yadda ake yi a Ebonyi. Idan kowane gwamna ya tsare jiharsa, to Najeriya za ta samu tsaro.”

- Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata Kalu ya wanke Tinubu kan rashin tsaro
Sanata Orji Uzor Kalu a zauren majalisar dattawa Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Kalu na son APC ta yi nasara a Abia

Sanata Kalu, wanda jigo ne a jam’iyyar APC, ya kuma sha alwashin mika jihar Abia ga APC a zaɓen 2027.

Ya ce zai yi aiki tukuru don sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu, tare da tabbatar da samun gwamnan APC a Abia.

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya bar duniya kwana 1 kafin bikin zagayowar ranar haihuwarsa

“Alex Otti abokina ne, amma zan kaɗa kuri’a ne ga jam’iyyata APC, kuma zan yi aiki domin nasararta. Abia za ta zama ta APC a 2027, kuma zan sadaukar da duk karfina wajen ganin APC ta yi nasara.”

- Sanata Orji Uzor Kalu

Tinubu zai canza sunan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto mai suna Toye Ebijomore, ya yi hasashe kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Fasto Toye Ebijomore ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna kafin karewar wa’adin mulkinsa.

Ya ce hasashen ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin wahayi game da makomar Najeriya da siyasar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng