'Shugaba Bola Tinubu zai Sanya wa Najeriya Sabon Suna'
- Wani fasto a Akure ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna kafin karewar wa’adinsa a mulki
- Faston ya ce za a kafa kawancen jam’iyyun adawa masu ƙarfi domin karɓe mulki a 2027, amma za a samu matsalolin da za su tarwatsa su
- Ya yi hasashen yalwar abinci a cikin shekarar 2026 tare da gargadin sauyin yanayin rashin tsaro a ƙasar, inda ya ce zai shafi jama'a da yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Wani fasto mai suna Toye Ebijomore ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna kafin karewar wa’adin mulkinsa, tare da tsallake duk wani shiri na siyasa da ake yi domin dakile shi.
Rahoto ya nuna cewa Faston ya bayyana hakan ne a cikin hasashensa na shekarar 2026 da ya gabatar a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Fasto Toye Ebijomore ya ce hasashen ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin wahayi game da makomar Najeriya da siyasar ƙasar nan.
Hasashen makomar Bola Tinubu a 2027
A cewar faston, za a samu gagarumin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun siyasa da nufin kwace mulkin Najeriya daga hannun APC a zaɓen shekarar 2027.
Sai dai ya ce wannan kawance ba zai daɗe ba, domin wasu masifu da rashin jituwar ra’ayi za su raunana haɗakar har ma su kai ga rugujewarsa.
Fasto Ebijomore ya ce duk da yunƙurin kawancen jam’iyyun adawa, jam’iyya mai mulki za ta cigaba da mulki bayan zaɓe mai zuwa.
Ya ƙara da cewa wata sabuwar jam’iyya mai ƙarfi za ta taso a gaba, wadda daga bisani za ta iya ƙwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki a wani lokaci nan gaba
Daily Nigerian ta rahoto cewa ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi biyayya ga umarnin Ubangiji ta hanyar kira a yi addu’ar ƙasa baki ɗaya domin kare martabar Najeriya.
Hasashen yalwar abinci a Najeriya
Faston ya kuma yi hasashen cewa a shekarar 2026, Najeriya za ta shiga yanayin yalwar abinci. Ya shawarci gwamnati da ta yi amfani da wannan dama wajen rage tsadar abinci da magunguna domin sauƙaƙa wa talakawa rayuwa.
Ya ce shekarar 2026 za ta kasance cike da yalwa da albarka, amma a lokaci guda za a fuskanci ƙarin ƙalubale da hare-hare kan mutane.
A cewarsa, waɗanda suka tsaya kan gaskiya da addu’a kuma suka dogara da kariyar Ubangiji ne kaɗai za su tsira daga waɗannan hare-hare.
Ya gargadi gwamnati da ta sanya ido kan mutanen da ke ɗaukar nauyin yaɗa ƙiyayya da kai hari ga manyan mutane masu mutunci, musamman malamai da fastoci.

Source: Facebook
Tinubu zai ba da tallafi a 2026
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo sabon shiri domin tallafawa talakawan Najeriya a shekarar 2026.
Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta zakulo mutane 1,000 a kowace mazaba a fadin Najeriya domin tallafa musu.
A karkashin sabon shirin, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kimamin 'yan Najeriya miliyan 10 ne za su samu tallafin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng

