Tarin 'Yan Ta'adda Sun Mamaye Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kona Shi Kurmus

Tarin 'Yan Ta'adda Sun Mamaye Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kona Shi Kurmus

  • Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta bayyana yadda wasu ’yan ta’adda dauke da makamai suka kai hari kan ofishin ’yan sanda na Ipele a daren sabuwar shekara
  • Rahotanni sun nuna cewa tsakanin 'yan ta'adda 20 zuwa 30 ne suka farmaki ofishin, suna harba bindigogi tare da amfani da abubuwan fashewa cikin dare
  • Biyo bayan lamarin, kwamishinan ’yan sandan jihar ya yi Allah-wadai da harin, yana mai tabbatar da cewa an fara farautar wadanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta fitar da karin bayani game da harin da wasu ’yan ta’adda suka kai kan ofishin ’yan sanda na Ipele da ke jihar, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

A cewar rundunar, harin ya faru ne a daren jajibirin sabuwar shekarar 2026, lokacin da maharan suka shiga yankin tare da kai farmaki kai tsaye kan ofishin ’yan sanda.

Ofishin 'yan sanda a jihar Ondo
Ofishin 'yan sanda da aka kaiwa hari a Ondo. Hoto: @breez919fm
Source: Twitter

NTA ta wallafa a X cewa rundunar ta ce duk da barnar da aka yi, babu asarar rai a yayin harin, lamarin da ta ce abin godiya ne duk da girman asarar da aka yi.

Yadda aka kai hari ofishin 'yan sanda

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, DSP Jimoh Abayomi, ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 9:41 na dare.

Kakakin rundunar ya ce rahotannin farko sun nuna cewa tsakanin mutum 20 zuwa 30 dauke da makamai ne suka afka ofishin ’yan sandan Ipele.

Abayomi ya ce maharan sun rika harba bindigogi tare da amfani da abubuwan fashewa, lamarin da ya haddasa mummunar barna ga ginin ofishin.

Sufeton 'yan sanda na kasa
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa ya kara da cewa an kona ginin gaba daya tare da lalata kayayyaki da muhimman abubuwan da ke cikin caji ofis din.

Ya kara da cewa duk da tsananin harin, babu wani jami’in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta cafke fiye da mutane 3,000 a Kano, kwamishina ya yi bayani

Matakan gaggawa da aka dauka

DSP Abayomi ya ce da zarar rundunar ta samu rahoton kiran gaggawa, aka tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa wurin. Tawagar ta kunshi jami’an ’yan sanda, sojoji, hukumar NSCDC da wasu jami’an tsaron sa-kai.

Sai dai ya bayyana cewa kafin isowar jami’an tsaron, maharan sun riga sun tsere daga wurin. Wannan ya sa jami’an tsaron suka fara bincike a yankin domin gano inda suka bi.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ondo, Adebowale Lawal, ya yi kakkausar suka kan harin, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan aiki da ya saba wa zaman lafiya da tsaron jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa an kaddamar samame na musamman domin kamo wadanda suka kai harin. Ya ce hukumomin tsaro suna aiki tare domin gano masu hannu a lamarin da kuma hana afkuwar makamancin haka a nan gaba.

'Yan ISWAP sun kai hari jihar Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'addan da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun kai wani mummunan hari jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin Amurka a Sokoto, mayakan ISWAP sun kai kazamin hari Yobe

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun raunata wani basarake, inda aka garzaya da shi asibiti yana samun kulawa bayan tafiyarsu.

A wani bangare na harin da suka kai, 'yan ta'addan sun farmaki wani asibiti, inda suka sace muhimman kayayyakin da ake aiki da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng