'Dan Majalisa a Amurka Ya Fadi Manufar Trump wajen Kawo Hari Najeriya

'Dan Majalisa a Amurka Ya Fadi Manufar Trump wajen Kawo Hari Najeriya

  • 'Dan majalisa a Amurka, Riley Moore, ya kare Shugaba Donald Trump kan matakin da ya dauka na kawo hare-hare a Najeriya
  • Riley Moore ya bayyana cewa ba a kawo hare-haren da nufin wargaza zaman lafiya a Najeriya ba, sai don samar da tsaro
  • 'Dan majalisar dokokin ya kuma bayyana amfanin da Kiristoci a Najeriya suka samu sakamakon hare-haren da aka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Wani dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya kare Shugaba Donald Trump kan hare-haren da ya ba da umarnin kawowa Najeriya.

Riley Moore ya ce hare-haren saman da Amurka ta kai kwanan nan a Najeriya an yi su ne domin kawo zaman lafiya da tsaro, ba domin jefa kasar cikin yaki ba.

Riley Moore ya kare Donald Trump kan harin da ya kawo Najeriya
Dan Majalisa a Amurka, Riley Moore Hoto: @RepRileyMoore
Source: Getty Images

'Dan majalisar na Amurkaya bayyana hakan ne ta wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Me dan majalisar ya ce kan harin Trump?

Riley Moore ya ce hare-haren da aka kai kan kungiyar ISIS a ranar Kirsimeti an yi su ne domin kare dubban Kiristoci da ke fuskantar munanan hare-hare da barazanar rasa rayukansu a Najeriya.

Ya kara da cewa aikin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya sake ba Kiristoci a Najeriya kwarin gwiwa.

“Shugaba Trump ba ya kokarin kawo yaki a Najeriya, yana kokarin kawo zaman lafiya da tsaro a Najeriya da kuma ga dubban Kiristocin da ke fuskantar mummunan tashin hankali da mutuwa."
“Hare-haren da aka kai kan ISIS a ranar Kirsimeti, tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya, sun bai wa Kiristoci a Najeriya kwarin gwiwa."

- Riley Moore

Kasar Amurka ta kawo hari Najeriya

Hare-haren na sojojin Amurka, wanda Trump ya sanar, ya ce sun kunshi kai farmaki cikin kwarewa kan sansanonin ISIS a jihar Sokoto.

Rundunar sojojin Amurka ta Afirka (AFRICOM) ta bayyana cewa an kashe 'yan ta'adda da dama yayin harin.

Kara karanta wannan

Martanin Tambuwal da sauran manyan 'yan siyasa kan harin Amurka a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da hadin gwiwar, tana mai cewa harin wani bangare ne na ci gaba da yaki da ta’addanci tsakanin kasashen biyu.

Sai dai wasu masu sukar matakin sun nuna damuwa cewa hakan na iya barazana ga ikon Najeriya da kuma rayukan fararen hula.

Riley Moore ya kare Donald Trump

Riley Moore ya mayar da martani kan masu sukar, yana mai cewa matakin ya zama dole domin dakatar da hare-haren da ake kai wa Kiristoci.

Riley Moore ya goyi bayan Trump kan kawo hari Najeriya
Dan majalisar dokoki a kasar Amurka, Riley Moore Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

'Dan majalisar ya bayyana cewa Shugaba Trump ya taba yin gargadi a baya kan “kisan gillar” Kiristoci a Najeriya.

Hare-haren sun biyo bayan ayyana Najeriya da Trump ya yi a matsayin “kasa mai damuwa ta musamman” kan zargin muzgunawa Kiristoci a kasar.

Mutane sun fara guduwa kan harin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsoron yiwuwar kawo hare-haren bama-bamai na Amurka ya sanya mutane sun fara tunanin barin kauyukansu.

Wasu daga cikinsu sun hangi jiragen yakin sojoji suna shawagi a sama na kusan mintuna 30 kafin daga bisani su ɓace.

Sun bayyana cewa hare-haren da Amurka ta kai a jihohin Sokoto da Kwara sun sanya su cikin firgici matuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng