Hankula Sun Girgiza bayan Bama Bamai Sun Tashi da Matafiya a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

Hankula Sun Girgiza bayan Bama Bamai Sun Tashi da Matafiya a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

  • Ana zargin 'yan bindiga da dasa bama-bamai a kan hanyar wani titi a jihar Zamfara wanda ya jawo asarar rayuka
  • Sau uku abubuwan fashewa suka tashi daban-daban a kan hanyar wadda mutane ke amfani da ita domin zirga-zirga
  • Shaidun gani da ido sun bayyana cewa fashe-fashen sun jawo asarar rayukan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon jerin fashe-fashe da suka auku a kan hanyar Dansadau a jihar Zamfara.

Fashe-fashen sun faru ne a ranar Asabar, 27 ga watan Disamban 2025, a yankin Mai Aya Aya, kafin mashigar Kwankelai a tsohuwar hanyar Dangulbi, kusa da kauyen Ruwan Dawa da Magamin Maitarko.

Bama-bamai sun kashe mutane a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin cewa ’yan bindiga ne suka dasa abubuwan fashewa (IEDs) a wurare uku daban-daban a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Halin da mazauna kauyen Sokoto ke ciki a yanzu bayan harin Amurka

Bama-bamai sun kashe mutane a Zamfara

Wani ganau, Malam Yunusa Isah, mazaunin kauyen Malele, ya ce fashewar farko ta kashe mutane hudu nan take.

“’Yan bindiga ne suka dasa bam din, kuma ya kashe mutane hudu. Cunkoson ababen hawa ya yi yawa sosai, ba ma iya isa daidai wurin da bam din ya tashi."

- Yunusa Isah

Ya kara da cewa fashewar bam ta biyu ta auku ne lokacin da wata tirela ta taka shi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.

Wani mazaunin Dansadau, Malam Nuhu Ibrahim Dansadau, ya ce fashewar farko da ta biyu sun hallaka mutane tara, yayin da ake ci gaba da tattara bayanan wadanda suka jikkata ko suka mutu a fashewa ta uku.

“Har yanzu muna tattara adadin asarar rayuka da ta auku a fashewa ta uku."

- Malam Nuhu Ibrahim

Ya kuma yi zargin cewa al’ummar Dansadau na fuskantar karuwar hare-haren ’yan bindiga tun bayan ziyarar Gwamna Dauda Lawal, yana mai cewa masu kai hare-haren na kokarin tsoratar da jama’a ne tare da dakile aikin kamfanin da ke gina hanyar Dansadau.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta kama gini mai hawa 22, akwai 'yan kasuwa a ciki

Ana zargin 'yan bindiga da dasa bam

Nuhu Ibrahim ya danganta lamarin da rikicin da ya faru a ranar Juma’a tsakanin wasu Fulani da mazauna Magami.

“Mutanen Magami sun yi sulhu da ’yan bindiga, amma jiya an hana ’yan bindiga sayar da shanunsu da suka sato a kasuwar Magami. Wannan mataki na iya tunzurasu su dauki wannan harin."
"Sannan kuma ba sa son kamfanin da ke aiki ya kammala aikin hanyar Dansadau da gwamna ya ba da kwangilarsa kwanan nan."

- Malam Nuhu Ibrahim

'Yan bindiga sun dasa bama-bamai a Zamfara
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun yi bayani

A halin da ake ciki, rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa wasu abubuwan da ake zargin IEDs ne suka fashe a kan hanyar Dansadau zuwa Magami.

Rundunar ta ce amma har yanzu ba a tantance ainihin adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

“Wasu abubuwa da ake zargin IEDs ne sun fashe a kan hanyar Dansadau–Magami, amma har yanzu muna tattara bayanai."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri

- DSP Yazid Abubakar

Bam ya tashi a Maiduguri

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin bam a wani masallaci da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din da misalin karfe 6:00 na yammaci a wani masallacin Gamboru a Maiduguri.

Dan kunar bakin waken ya shiga masallacin ne a boye kafin daga bisani ya tayar da bam din wanda ya jawo asarar rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng