Bayan Trump, Netanyahu Ya Tsoma Baki a Najeriya kan Zargin Kashe Kiristoci
- Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan zargin kisan Kiristoci da Amurka ta ce ana yi a Najeriya a kwanakin baya
- Netanyahu ya yi ikirarin cewa a Isra’ila ce kasa daya tilo a Gabas ta Tsakiya da Kiristoci ke yin addininsu cikin ’yanci ba tare da tsoro ba
- Ya kwatanta halin da Kiristoci ke ciki a wasu yankuna da raguwar adadinsu, yana danganta hakan da tsangwama da wariya da ake musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Israel – Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi suka kan zargi maras hujja kan kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan lamari abin Allah wadai ne.
Netanyahu ya bayyana hakan ne a cikin sakon Kirsimetinsa da ya fitar, inda ya jaddada cewa kai hari kan Kiristoci ko mabiya kowane addini ba abu ne da duniya za ta amince da shi ba.

Source: Getty Images
Tribune ta rahoto ya ce dole ne a kawo karshen tashe-tashen hankula da korar Kiristoci daga muhallansu a fadin duniya.
Maganar Netanyahu kan Najeriya
A cewar Netanyahu, hare-haren da kungiyoyin ’yan bindiga ke kai wa Kiristoci a Najeriya na haddasa asarar rayuka da raba al’umma da muhallansu.
Ya ce irin wadannan ayyuka suna barazana ga zaman lafiya da hadin kan addinai, kuma ba su dace da ka’idojin bil’adama ba.
Firaministan ya jaddada cewa duk wani nau’i na tsangwama ko kisan kiyashi bisa addini dole ne a dakatar da shi, yana mai cewa lokaci ya yi da duniya za ta dauki wannan lamari da muhimmanci.
Rayuwar Kirostoci a kasar Isra'ila
Netanyahu ya bayyana Isra’ila a matsayin kasa daya tilo a Gabas ta Tsakiya inda Kiristoci ke samun cikakken ’yanci na yin addininsu.
Ya ce a Isra’ila, Kiristoci na gudanar da bukukuwansu cikin walwala, suna kuma samun girmamawa daga gwamnati da al’umma baki daya.

Source: Getty Images
A cewarsa, adadin Kiristoci a Isra’ila na ci gaba da karuwa, sabanin abin da ke faruwa a wasu kasashen yankin a halin yanzu.
Batun alamomin Kiristanci a Urushalima
Punch ta wallafa cewa Netanyahu ya tabo batun mutunta alamomin addinin Kirista, yana cewa birnin Urushalima na raba kayan Kirsimeti a hukumance duk shekara tsawon shekaru 20.
Sai dai ya kwatanta hakan da wani lamari a garin Jenin, inda aka ya ce an kona wasu abubuwan da suka shafi Kirsimeti a cocin Holy Redeemer.
A cewarsa, wannan bambanci ne tsakanin yadda Isra’ila ke kare Kiristoci da kuma yadda ake tsangwamar su a wasu yankuna.
Netanyahu ya kammala da aika sakon barka da Kirsimeti ga Kiristoci a duniya, yana mai cewa Isra’ila za ta ci gaba da tsayawa tare da su a duk inda suke fuskantar tsangwama.
Tinubu ya taya Kiristoci murna
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya Kiristoci murnar ranar Kirsimeti na shekarar 2025.
Bola Tinubu ya bukaci 'yan kasa su hada kai tare da mutunta bambancin da ke tsakaninsu, musamman a halin yanzu.
Gwamnonin Najeriya a jihohin da suka hada da Delta, Sokoto, Katsina da sauransu sun bi bayan Tinubu wajen taya su murna.
Asali: Legit.ng


