Abubuwan da Tinubu, Gwamnoni da NLC Suka Fada kan Bikin Kirsimetin 2025

Abubuwan da Tinubu, Gwamnoni da NLC Suka Fada kan Bikin Kirsimetin 2025

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin kare ’yancin addini tare da kiran ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da juna a bikin Kirsimeti
  • Gwamnonin jihohi sun yi kira ga jama’a da su rungumi kauna, hadin kai da hakuri duk da kalubalen tattalin arziki da tsaro da ake fama da shi
  • Kungiyar kwadago ta NLC ta yi korafi kan matsin tattalin arziki da harajin da aka iya kara wahalar rayuwa ga ’yan kasa a sakon da ta fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – A yayin da Kiristoci ke bikin Kirsimeti a 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnonin jihohi sun yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da son juna.

Sakon Kirsimetin shugabannin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin tattalin arziki da kalubalen tsaro, inda aka jaddada muhimmancin juriya da fahimtar juna.

Kara karanta wannan

Atiku da NBA sun fadi hadarin da suka gani a dokar harajin Tinubu ta 2026

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na addu'a. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a wani sako da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Sakon Tinubu na ranar Kirsimeti

A sakon Kirsimetin da ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana cewa juriya da mutunta addinai su ne ginshikan hadin kan kasa. Ya ce babu wani dan Najeriya da ya kamata ya sha wahala ko rasa ransa saboda addininsa.

Shugaban kasar ya ce kauna da son bil’adama ne jigon manyan addinai, kuma ya kamata wadannan dabi’u su ci gaba da hada kan ’yan Najeriya duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Tinubu ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ’yancin kowane dan kasa na yin ibada cikin walwala da mutunci, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Sakon Kirsimeti daga gwamnonin Najeriya

Punch ta wallafa cewa a jihohi daban-daban, gwamnonin sun yi amfani da sakonnin Kirsimeti wajen jaddada kauna da bukatar hadin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bukaci al’ummar jiharsa da su rungumi rayuwar da ta dace da koyarwar Annabi Isa domin samun zaman lafiya da ci gaba.

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta na yawabi. Hoto: Delta State Government
Source: Twitter

A Katsina, Gwamna Mallam Dikko Radda ya taya Kiristoci murna tare da kira da su yi tunani kan darussan kauna da sadaukarwa, yana mai tabbatar da kare ’yancinsu na yin ibada.

Haka nan gwamnonin Bayelsa, Adamawa, Ondo da Sokoto sun yi kira ga jama’a da su dage da addu’o’i, hadin kai da hakuri duk da kalubalen tattalin arziki da tsaro da ake fuskanta.

Sakon Kirsimetin 'yan kwadago

Kungiyar Kwadagon Najeriya ta bayyana cewa duk da murnar Kirsimeti, ma’aikata na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki da manufofi da ke kara musu wahala.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce akwai bukatar adalci a tsarin haraji domin rage radadin da ’yan kasa ke ciki a halin yanzu.

A cewarsa, hadin kai da fahimtar juna za su taimaka wajen shawo kan kalubalen Najeriya, amma dole ne a kula da walwalar ma’aikata da talakawa.

Kwankwaso ya yi kira ga Tinubu

Kara karanta wannan

Za a fara alkunut, malamai sun yi wa Amurka martani kan Shari'a da Hisbah

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci Bola Tinubu ya inganta tsaron Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewa rashin kokari daga bangaren shugabannni na cikin abubuwan da ke kara dagula matsalar tsaro.

Ya kara da cewa idan ya samu shugabancin Najeriya zai dauki sojoji sama da miliyan 1 domin samar da cikakken tsaro a kasa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng