Sojoji Sun Yi Bayani kan Harin Bam da Ya Kashe Musulmai a Masallacin Borno

Sojoji Sun Yi Bayani kan Harin Bam da Ya Kashe Musulmai a Masallacin Borno

  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin bam masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri yayin sallar Magariba, a ranar Laraba, 24 ga Disamba, 2025
  • Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani dan kunar bakin wake daga kungiyar Boko Haram ne ya tayar da bam din, inda aka samu raunuka masu yawa
  • Biyo bayan lamarin, dakarun rundunar sojin Najeriya sun ce sun dauki matakan gaggawa tare da kara tsaurara tsaro domin hana sake aukuwar irin wannan hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Rundunar Sojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai ta tabbatar da fashewar bam a masallacin da ke cikin kasuwar Gamboru a birnin Maiduguri, yayin da masu ibada ke tsaka da gudanar da sallar Magariba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na yamma, abin da ya haddasa firgici da tashin hankali a tsakanin jama’a da ke wurin.

Wajen da aka kai hari a masallacin Borno
Mutane da jami'an tsaro a masallacin da aka tayar da bam a Borno. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa sun bayyana cewa bayan faruwar lamarin, an hanzarta daukar matakai domin ceton wadanda abin ya shafa da kuma tabbatar da tsaron yankin.

Bayanin rundunar sojin Najeriya

Jami’in yada labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa rundunar sojin ta samu rahoton ne a lokacin da ake tsaka da sallar Magariba a masallacin da ke kasuwar Gamboru.

A cewarsa, binciken farko-farko ya nuna cewa wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram ne ya kai harin ta hanyar tayar da bam din da ya daura a jikinsa, wanda ya kashe shi nan take tare da wasu fararen hula a wajen.

Ya kara da cewa wannan hari na kunar bakin wake ya sake nuna yadda kungiyoyin ta’addanci ke kokarin tayar da hankalin al’umma musamman a wuraren taruwar jama’a.

Matakan gaggawa da aka dauka

Laftanar Kanal Sani Uba ya ce dakarun soji tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, sashen kwance bama-bamai, da sauran hukumomin tsaro sun kai dauki cikin gaggawa bayan harin.

Kara karanta wannan

'An kusa gama gyara lantarkin Najeriya,' Ministan makamashi ya yi albishir

An killace yankin gaba daya domin hana sake afkuwar wata barazana, tare da kwashe wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Maiduguri da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin samun kulawar likitoci.

Haka kuma, gwamnatin jihar Borno da hukumar NEMA sun shiga aikin bayar da agaji ga wadanda abin ya shafa, musamman wajen daukar marasa lafiya da tallafawa iyalan da lamarin ya rutsa da su.

Kiran sojoji da gargadi ga jama’a

Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta kara kaimi wajen sanya ido da tsaurara tsaro a Maiduguri da kewaye, musamman a wannan lokaci da ake samun yawaitar tarukan jama’a.

An shawarci mazauna birnin da su kasance masu taka-tsantsan, su guji wuraren cunkoso, tare da kai rahoton duk wani abu ko motsi da ke janyo shakku ga ofishin tsaro mafi kusa.

Shugaban sojojin kasan Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya da shugabansu. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Rundunar ta kuma jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da tabbatar wa al’umma cewa sojoji ba za su sassauta ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin Arewa maso Gabas.

Barnar da bam ya yi a masallacin Borno

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta ce akalla fararen hula hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon hari bam a masallacin Borno.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Tanka makare da fetur ta tarwatse a tsakiyar gidan mai a Bauchi

Jimillar mutane 32 ne suka samu raunuka daban-daban, inda wasu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali yayin da sauran ke samun sauki a karkashin kulawar likitoci.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da bibiyar yanayin lafiyar wadanda suka jikkata domin tabbatar da cewa an ba su kulawar da ta dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng