Yadda 'Yan Najeriya Suka Biya Biliyoyi a matsayin Kudin Fansa cikin Shekara 1

Yadda 'Yan Najeriya Suka Biya Biliyoyi a matsayin Kudin Fansa cikin Shekara 1

  • Matsalar rashin tsaro ta sanya 'yan bindiga suna yin garkuwa da mutane domin neman makudan kudaden fansa kafin a sake su
  • An fitar da wani rahoto wanda ya bayyana biliyoyin da 'yan Najeriya suka batar wajen biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa
  • Yankin Arewa maso Yamma na kan gaba wajen fuskantar matsalar satar mutane don neman kudin fansa da kaso mafi tsoka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Masu garkuwa da mutane sun karɓi makudan kudade a matsayin kudin fansa a cikin shekara.

Masu garkuwa da mutanen sun karbi akalla Naira biliyan 2.57 a matsayin kuɗin fansa daga watan Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.

'Yan bindiga sun karbi kudaden fansa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin rahoton da SBM Intelligence ta fitar.

Rahoton wanda aka fitar a ranar 19 ga Disamba, 2025, ya yi nazari kan manyan al’amuran tattalin arziki da siyasa da ke tsara makomar Afirka a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

N58.47tn: Majalisa ta fara tafka muhawara kan kasafin 2026 da Tinubu ya gabatar

Kudin fansa: 'Yan Najeriya sun biya N2.5bn

Hakazalika, rahoton ya bayyana cewa a cikin watanni 12 ɗin da aka duba, masu garkuwa da mutanen sun nemi kimanin Naira biliyan 48 a matsayin kudin fansa.

SBM Intelligence ta ce alkaluman sun nuna cewa garkuwa da mutane a Najeriya ta rikide zuwa wata sana’a mai tsari da nufin riba.

Rahoton ya ce sana'ar na bunkasa sakamakon raunin shugabanci, faɗaɗɗun yankunan karkara marasa tsaro, da tabarbarewar yanayin tsaro a yankuna da dama na kasar.

Premium Times ta ce a cewar rahoton, akalla mutane 4,722 aka sace a cikin lamuran garkuwa da mutane 997 a lokacin da aka duba, yayin da akalla mutane 762 suka mutu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da makamantan tashin hankali.

Duk da cewa bukatar kudin fansa ta karu sosai idan aka auna da Naira, SBM Intelligence ta lura cewa adadin kuɗin da masu garkuwa suka samu a zahirin darajar Dala bai yi yawa ba, sakamakon faduwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Fetur: Man da Najeriya ta dogara da shi ya ba ta kunya a hasashen kudin shigan 2025

Binciken ya ce Naira biliyan 2.57 da aka biya a matsayin kudin fansa a wannan lokaci na daidai da kusan Dala miliyan 1.66, wanda da kadan ya wuce Dala miliyan 1.13, daidai da Naira miliyan 653.7 da aka tattara a shekarar 2022.

Ana yawan sace mutane a yankin Arewa

Arewa maso Yamma ya ci gaba da zama cibiyar garkuwa da mutane a Najeriya, inda aka samu satar mutane sau 425, wato kashi 42.6 cikin 100 na dukkan sace-sacen da suka faru a faɗin kasar.

An kuma sace mutane 2,938 a yankin, wanda ya kai kashi 62.2 cikin 100 na jimillar waɗanda aka yi garkuwa da su.

Jihar Zamfara ce ta fi yawan waɗanda aka sace da mutum 1,203, sai Kaduna da Katsina suka biyo baya.

SBM Intelligence ta danganta yawaitar garkuwa a yankin da faɗaɗɗun yankunan karkara marasa kyakkyawan shugabanci da kuma karfafa hanyoyin ’yan bindiga da ke ba su damar gudanar da manyan ayyuka ba tare da turjiya ba.

Ana yawan sace mutane a Najeriya
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Akwai dama-dama a Kudu maso Yamma

A ɗaya ɓangaren kuma, Kudu maso Yamma ne ya fi karancin samun garkuwa da mutane, inda ya kaso 5.3 cikin 100 kacal.

Hakazalika yankin ya samu kaso 3 cikin 100 na adadin mutanen da aka sace a lokacin da aka kammala rahoton.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya masu zuwa Mauludi a Plateau

'Yan bindiga sun sace matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu matafiya a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron Maulidi a karamar hukumar Wase.

Daga cikin mutanen da 'yan bindigan suka sace har da jinin sarauta da malamin addinin da ke jagorantar tafiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng