Yadda Gwamna Makinde Ya Watsawa Tinubu Kasa a Ido bayan Ya Nemi Wata Alfarma
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tuna baya kan wata alfarma da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nema a wajensa
- Seyi Makinde ya bayyana cewa bai amince da bukatar da shugaban kasar ya gabatar masa ba saboda shi dan jam'iyyar PDP ne
- Gwamna Makinde ya bayyana cewa Wike ya taba gayawa Tinubu cewa zai hana abubuwa tafiya yadda ya kamata a jam'iyyar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana yadda ya ki amincewa da bukatar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar masa.
Gwamna Makinde ya ce ya ki amincewa da bukatar Tinubu ta ya taimaka wajen hada kan jam’iyyar APC a jihar Oyo, yana mai nuna amincinsa ga PDP.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai da aka yi a ranar Talata, 23 ga watan Disamban 2025 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Wace alfarma Tinubu ya nema wajen Makinde?
Ya ce batun ya taso ne bayan wata tattaunawa da ya yi da Shugaba Tinubu kan naɗin minista daga jihar Oyo bayan kafa majalisar ministocin tarayya.
A cewarsa, shugaban kasar ya yi masa magana kai tsaye inda ya ce:
“Ya ce mini, ‘Seyi, kai ne nake so ka taimaka mini wajen hada kan APC a jihar Oyo’.”
Sai dai Makinde ya ce ya ki yarda kai tsaye, yana mai jaddada cewa ba zai iya yin abin da ya saɓa wa jam’iyyarsa ba.
“Na ce masa, ‘A’a ranka ya daɗe, ba zan iya taimaka maka wajen hada kan APC a jihar Oyo ba, domin ni ɗan PDP ne’."
- Gwamna Seyi Makinde
Makinde ya yi zargi kan Wike
Gwamnan ya kuma ce ya halarci wani taro da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana a fili cewa yana da niyyar marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Gwamnan da ke takun saka da Wike a PDP ya sha alwashin abin da zai yi kafin zaben 2027
"Na kasance a wani taro tare da shugaban kasa da Wike. Ina faɗin wannan a fili. Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ma yana wurin, tare da wasu mutane kaɗan. Sai Wike ya ce wa shugaban kasa, ‘Ranka ya daɗe, zan hana PDP motsi dominka har zuwa 2027’.”
"Na yi matukar mamaki. Da muka tashi muka fita baranda, sai na ce masa, ‘Wike shin mun amince da wannan ne?’”
- Gwamna Seyi Makinde

Source: Facebook
Makinde zai kare dimokuradiyya
Gwamna Makinde ya jaddada cewa duk da cewa Wike na da ’yancin goyon bayan Shugaba Tinubu, shi kuma ba zai shiga duk wani tsari da zai raunana adawa ko barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
"Babban maganar ita ce Wike yana so ya goyi bayan shugaban kasa a 2027, babu laifi. Wannan 'yancinsa ne."
"Amma mu ma da muke son tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da wanzuwa a Najeriya, kada mu koma tsarin jam’iyya ɗaya tilo, kuma muna so PDP ta rayu. Ya kamata ya bar mu mu yi abin da mu ka ga ya fiye mana."
- Gwamna Seyi Makinde
Gwamna Makinde zai yi zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya shirya gudanar da zabe kafin ya bar mulki.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa zai gudanar da zaben kananan hukumomi kafin ya bar mulki a shekarar 2027.
Makinde ya nuna cewa wa'adin shugabannin kananan hukumomin jihar na yanzu zai kare ne a cikin shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

