An Zo Wajen: Shugaban EFCC Ya Fallasa Hanyar da Gwamnoni Ke Sace Dukiyar Jama'a
- Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya koka kan yadda ake karkatar da kudaden jama'a
- Ola Olukoyede wanda ya shiga ofis a 2023 ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi na sace kudaden tsaro da ake warewa duk wata
- Shugaban na EFCC ya bayyana cewa matsalar cin hanci da rashawa ta zama musabbabin tabarbarewar rashin tsaro a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi zargi kan wasu gwamnoni.
Shugaban na EFCC ya zargi wasu gwamnonin jihohi da karkatar da biliyoyin Naira daga kudaden tsaro da ake warewa duk wata.

Source: Twitter
Shugaban EFCC ya yi zarge-zarge
Jaridar The Cable ta ce shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata lakcar shekara-shekara, a ranar Juma'a, 19 ga watan Disamban 2025.
An shirya lakcar ne a sansanin sojojin sama na Sam Ethnan, da ke a Ikeja, jihar Legas.
Ya ce sau da yawa ana mayar da kudaden zuwa kudin kasashen waje, sannan a ajiye su a kasashen waje maimakon a yi amfani da su wajen bunkasa tsaro.
Ola Olukoyede ya jaddada cewa cin hanci da rashawa shi ne babban musabbabin tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Shugaban na hukumar EFCC ya ce kudaden da aka ware domin tsaro ko rage talauci, amma aka sace su, ana amfani da su ne wajen karfafa ’yan bindiga, masu tayar da kayar baya da masu tsattsauran ra’ayi.
Gwamnoni na karkatar da kudaden tsaro
Da yake yin misali da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, Olukoyede ya ce EFCC ta gano yadda ake zargin an karkatar da sama da Naira biliyan 4 daga kudaden tsaro.

Source: Facebook
"Gwamnonin jihohi na karɓar biliyoyin Naira duk wata a matsayin kudaden tsaro ba tare da bayyana yadda aka yi da su ba."
“Wadannan kudade, maimakon a zuba su wajen inganta tsarin tsaro, sau da yawa suna karewa a wajen 'yan canji, inda ake mayar da su kudin waje a kai su kasashen waje, ko kuma a batar da su a wuraren da ba su da alaka da tsaro."
“Da ace an kashe wadannan kudade yadda ya dace, da yanayin tsaron Anambra da jihohin da ke makwabtaka da ita ya fi yadda yake a yau.”
- Ola Olukoyede
Jami'an EFCC sun kai samame gidan Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), sun kai samame wani gidan tsohon Antoni Janar kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami.
Kafin rufe gidan da ke birnin Abuja, motoci da dama na EFCC tare da jami’ai ɗauke da makamai ne suka mamaye shi.
Matakin na EFCC dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tsananta bincike kan zarge-zargen da ake yi wa tsohon Ministan na shari'a a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

