Natasha Ta Yi Wa Akpabio Shagube bayan Ya Mika Kokensa ga Tinubu

Natasha Ta Yi Wa Akpabio Shagube bayan Ya Mika Kokensa ga Tinubu

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya fito ya nemi alfarma wajen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Godswill Akpabio ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sake duba umarnin da ya bayar na janyewa sanatoci 'yan sanda
  • Sai dai, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fito ta yi wa shugaban majalisar dattawan shagube kan rokon da ya yi

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta mayar da martani kan rokon da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Akpabio dai ya roki Shugaba Tinubu da ya sake duba matakin janye ’yan sandan da ke tare da ’yan majalisa.

Sanata Natasha ta yi wa Akpabio shagube
Sanata Natasha Akpoti da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Natasha H Akpabio, Godswill Obot Akpabio
Source: Twitter

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi martanin ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

Ta bayyana cewa imaninta da goyon bayan al’ummarta ne ainihin kariyarta.

Wane martani Natasha ta yi wa Akpabio?

Kalamanta na nuna alamun martani ne kai tsaye ga kalaman Akpabio a zaman haɗin gwiwar majalisar tarayya da aka yi ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025 lokacin da Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kuɗi na 2026.

Da take ambato roƙon Akpabio ga shugaban lasa, ta rubuta cewa:

"Wani ya ce wasu sanatoci ba za su iya komawa gida a wannan hutu ba, don Allah a sake duba tsarin tsaro.”
"Lokacin da ka janye min jami'an tsaro a cikin wannan dakatarwar da ba ta halatta ba fa? Allah Maɗaukakin Sarki, ta hannun kaunatattun al’ummata na Kogi ta Tsakiya, su ne tsarona."

A tuna cewa an dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida daga Majalisar Dattawa tare da kwace mata dukkan hakkoki, bisa zargin rashin da’a a zauren majalisar.

Akpabio ya yi roko a wajen Tinubu

Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa a zaman ranar Juma’a cewa wasu ’yan majalisa na iya fuskantar barazanar tsaro bayan aiwatar da umarnin Shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane.

Kara karanta wannan

Akpabio ya goyi bayan kashe 'yan bindiga masu garkuwa da mutane

A baya dai, a watan Nuwamba, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a mayar da ’yan sandan da aka raba wa ’yan siyasa, ’yan kasuwa da sauran manyan mutane zuwa ayyukan tsaro na asali domin tinkarar matsalar rashin tsaro da ƙarancin jami’ai a muhimman yankuna.

Wannan mataki na daga cikin kokarin karfafa tsaron jama’a da cike gibin karancin jami’an tsaro.

Akpabio ya nemi bukata wajen Tinubu
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Sai dai Akpabio ya yi gargaɗin cewa wannan mataki na iya barin wasu ’yan majalisa cikin hatsari, musamman a lokacin hutun bukukuwa.

"Yayin da kake umartar hukumomin tsaro su janye ’yan sanda daga muhimman wurare, wasu mambobin majalisar tarayya sun ce na sanar da kai cewa ba za su iya komawa gida ba, saboda suna fargabar a kama su."
"Saboda haka muke roƙon shugaban kasa da ya sake duba wannan mataki.”

- Sanata Godswill Akpabio

Akpabio ya goyi bayan kashe masu garkuwa da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya goyi bayan hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane.

Godswill Akpabio ya ce a shirye majalisar dattawa take ta mara wa matakan da za su ƙarfafa tsaro, ciki har da hukuncin kisa ga masu aikata garkuwa da mutane.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa an daidaita laifin garkuwa da mutane da ta’addanci a cikin sababbin matakan doka da aka dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng