Obaseki: Tsohon Gwamna Ya Ware Wasu 'Yan Siyasa, Ya Ce Sun Shiga Uku a Wurin Allah

Obaseki: Tsohon Gwamna Ya Ware Wasu 'Yan Siyasa, Ya Ce Sun Shiga Uku a Wurin Allah

  • Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi nasiha da tunawa shugabanni amanar Allah da ta al'ummar da suka zabe shi
  • Obaseki ya bayyana cewa duk wani dan siyasa da ya samu mulki amma ya ci amanar al'umma, to zai dandana kudarsa a wurin Allah
  • Ya ce bai taba nadamar matakan da ya dauka lokacin da yake matsayin gwamnan Edo ba, ya ce zai sake maimaita su idan ya samu dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi gargaɗi cewa duk wani ɗan siyasa da ya samu mulki amma ya yi amfani da shi don amfanin kansa da na kusa da shi kawai, zai gamu da fushin Allah.

Kara karanta wannan

An lakaɗawa Kansila duka kan zargin ba shi kuɗi ya mari na kusa da Gwamna

A cewarsa, shugabannin da ke neman mulki domin su wadatar da kansu da abokansu bayan sun lashe zaɓe, sun ci amanar Allah da kuma al’umma kuma Ubangiji ba zai kyale su ba.

Tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki wanda ya bar ofis a 2024 Hoto: @GovernorObaseki
Source: Facebook

Godwin Obaseki ya gargadi 'yan siyasa

Obaseki ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi tsokaci kan shugabanci, siyasa da shekarun da ya shafe yana mulkin jihar Edo.

“Idan ka shiga siyasa ne kawai don ka samu mulki, kuma bayan ka samu wannan mulki ka yi amfani da shi don kanka, abokanka da na kusa da kai, to Allah zai hukunta ka a ranar Lahira.
“Mulki kyauta ce daga Allah, kuma yana da manufa. Idan Allah ya ba ka iko amma ba ka yi amfani da shi wajen bauta masa ta hanyar yi wa jama’a hidima ba, to ka rasa ma’anar shugabanci.”

- Godwin Obaseki.

Obaseki ya yi nadamar mulkinsa a Edo?

Tsohon gwamnan ya ce ba ya nadamar duk wani mataki da ya ɗauka a lokacin mulkinsa, yana mai jaddada cewa dukkan shawarwarin da ya yanke ya yi su ne don amfanin al’ummar Edo.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi

“Ba ni da nadama game da lokacin da na yi a ofis. Idan aka ba ni dama a karo na biyu, ba zan sauya komai ba. A maimakon haka, zan sake yin abubuwan nan, zan yi saurin yinsu fiye da da,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya kuma yi gargadi kan rushe shirye-shiryen da gwamnatocin da suka gabata suka kafa, yana mai cewa irin hakan na cutar da talakawa ne kawai.

Obaseki.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki lokacin yana kan gadon mulki Hoto: Godwin Obaseki
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a ƙarshe, Obaseki ya tambayi lamirin shugabannin da ke jin daɗin mulki alhali jama’a na fama da yunwa da wahala.

“Ta yaya mutum zai samu mulki yau, ya yi barci lafiya, ya yi farin ciki, alhali yana ganin mutane da yawa ba su da abin ci kuma suna shan wahala? Mene ne manufar mulki idan ba ka fahimci dalilin da Allah ya ba ka iko ba?” in ji shi.

Gwamnan Edo ya zargi wasu 'yan siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro musamman ta garkuwa da mutane da ake fama da ita.

Gwamna Monday Okpebholo ya ce masu garkuwa da mutane na kai hare-hare ne don su yi wa Shugaba Bola Tinubu barazana da tsoratarwa.

Okpebholo ya nuna cewa akwai hannun 'yan siyasa dumu- dumu kan matsalar garkuwa da mutane, yana mai cewa sun biyo wannan hanya nw don cimma burinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262