Ta Kara Tsami Tsakanin Malami da EFCC bayan Ya Kwashe Kwamaki a Tsare

Ta Kara Tsami Tsakanin Malami da EFCC bayan Ya Kwashe Kwamaki a Tsare

  • Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC)
  • Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana ci gaba da tsare tsohon Ministan ne saboda ya gaza cika sharuddan belin da aka gindaya masa
  • Sai dai, Abubakar Malami ta hannun hadiminsa ya zargi hukumar da kin gayawa jama'a gaskiyar abin da ya faru ta hanyar cewa ya gaza cika sharuddan samun beli

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda ke tsare, ya sake yin zargi kan hukumar yaki da cin hanci da sashawa ta kasa (EFCC).

Abubakar Malami ya zargi EFCC da hana shi damar cika sharuddan beli da aka gindaya masa, yana mai cewa sharuddan belin sun yi tsauri kuma suna da wahalar cikawa.

Kara karanta wannan

"Ba ka cika sharudda 5 ba," EFCC ta maida zazzafan martani, ta yi kaca kaca da Malami

Malami ya yi zargi kan hukumar EFCC
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce mai taimaka masa a harkokin yaɗa labarai, Muhammed Bello Doka, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Disamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami ya musanta maganar hukumar EFCC

Ya ce ikirarin EFCC na cewa Malami ne ya hana kansa beli saboda rashin cika sharuddan da aka gindaya masa ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, sharuddan belin dabara ce ta ci gaba da tsare shi, ganin cewa ba abu ne mai sauƙi ba a samo manyan sakatarorin na tarayya da ke karkashin binciken gwamnati domin su tsaya masa.

“EFCC tana amfani da irin waɗannan sharudda ne da gangan domin tsawaita tsare shi, sannan kuma ta ce shi ne ya ki neman beli."

"Tun farko, Malami ya kasance a shirye ya cika dukkan sharuddan belin, amma hukumar ta hana shi damar yin hakan."

- Muhammed Bello Doka

Kara karanta wannan

'Yana kan daidai': Gumi ya goyi bayan Matawalle, ya fadi tasirinsa a Zamfara

Malami ya ce ba ya tsoron bincike

Dangane da zargin cewa yana kokarin gujewa bincike, Muhammed Bello Doka ya ce tsohon Ministan na Shari’a mutum ne mai bin doka da oda, kuma bai taɓa yin yunkurin gujewa bincike ba.

Malami ya ce EFCC ta ki ba shi damar samun beli
Abubakar Malami na jawabi a wajen taro Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Ya kara da cewa irin waɗannan kalamai ba daga Malami suka fito ba, illa daga hukumar EFCC.

Hakazalika, ya kuma yi kira ga hukumar EFCC da ta yi adalci ta hanyar gabatar da sharuddan beli masu yiwuwa a cika, tare da daina amfani da kafafen yaɗa labarai wajen cewa Malami ya ƙi amsar beli.

ADC ta zargi EFCC kan Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya, ta harzuka kan matakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta dauka na soke belin da ta ba tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.

ADC ta ce bisa dukkan hujjojin da ke akwai, Malami bai karya ko ɗaya daga cikin sharuddan belin da aka ba shi tun farko ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin EFCC na kokarin dakile shirin Malami na neman takarar gwamna a 2027

Hakazalika, ADC ta kuma yi zargin cewa EFCC ta soke belin Abubakar Malami ne saboda harkokinsa na siyasa wanda ya kunshi shirin neman kujarar gwamnan Kebbi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng