Gwamna Bago Ya Goyi bayan Wa'adi 1 a Mulki, Ya Fadi Amfaninsa

Gwamna Bago Ya Goyi bayan Wa'adi 1 a Mulki, Ya Fadi Amfaninsa

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya nuna rashin gamsuwa da tsarin wa'adi biyu a kan karagar mulki
  • Bago ya bayyana cewa tsarin yana kawar da hankalin shugabanni wajen yin abin da ya dace lokacin da suke kan madafun iko
  • Gwamnan ya nuna goyon baya ga tsarin wa'adi daya a kan mulki, inda ya nuna amfanin da hakan yake da shi

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin wa’adi ɗaya ga gwamnonin jihohi domin samun kyakkyawan shugabanci.

Gwamna Bago wanda ya shafe shekara biyu kacal a zangonsa na farko, bai bayyana tsawon lokacin da wa’adi guda ɗaya zai ɗauka ba, haka kuma bai fayyace shekarar da za a fara aiwatar da tsarin ba.

Gwamna Bago na son tsarin wa'adi daya a mulki
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Bago ya bayyana hakan ne yayin rantsar da sababbin kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu, manyan sakatarori da mambobin wasu hukumomi da kwamitoci.

Kara karanta wannan

Abba ya yi ta maza, ya murkushe yunkurin Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Bago ya ce kan wa'adi daya?

Gwamna Bago ya ce neman wa’adi na biyu na zama babban cikas wajen ɗaukar muhimman matakai da za su ciyar da jihar gaba, jaridar Daily Trust ta dauko labarin.

“Akwai wasu matakai da ya kamata na ɗauka domin ciyar da jihar nan gaba, amma bani da ƙarfin halin ɗaukarsu saboda tsoron cewa hakan zai shafi nasarata a zaben 2027."
"Misali, akwai wasu da suka fadi jarabawa kuma ya kamata a hukunta su ta wata hanya, amma ba a yi hakan ba saboda burin neman wa’adi na biyu.”
“Ni mai goyon bayan wa’adi guda ɗaya ne ga gwamnonin jihohi. Komai a jihar Neja an maida shi siyasa, kuma hakan na hana ɗaukar matakai masu ƙarfi."
"Akwai wasu mutane da nake son kora, amma ba zan iya ba. A matsayina na gwamna, hankalina ya fi karkata ga neman wa’adi na biyu, sakamakon haka shugabanci na shan wahala."

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna Fubara ya yi wa Tinubu alkawari kan zaben 2027

"Wannan ne ya sa wa’adi guda ɗaya ya fi, domin daga farko har karshe za ka mai da hankali kan aiki.”

- Gwamna Umaru Bago

Gwamna Bago ya soki tsarin wa'adi biyu a mulki
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Gwamna Bago ya ba da shawara

Gwamna Bago ya kuma yi kira ga waɗanda aka rantsar da su da su rungumi sabuwar manufar “New Niger Agenda”, domin ciyar da jihar gaba a kowane fanni na rayuwa.

“Bai kamata a nuna wariya ga kowa ba saboda yankin da ya fito, addininsa ko asalinsa. Dole ne mu gina sabuwar jihar Neja inda ɗan talaka zai iya zama wani abu. Wannan lokaci ne na komawa kan turba mai kyau domin gina sabuwar jihar Neja.”

- Gwamna Umaru Bago

Sai dai gwamnan bai bayyana ma’aikatu ko ofisoshin da sababbin kwamishinonin za su jagoranta ba, yana mai alkawarin cewa zai sanar da hakan cikin mako guda.

Gwamna Bago ya koka kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro.

Gwamna Bago ya ce masu bada bayanai na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ’yan ta’adda damar kai hare-hare.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Hakazalika, Gwamna Bago ya nemi a ɗauki tsauraran matakai a kansu domin rage matsalar rashin tsaro a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng