Ganduje na Fuskantar Barazanar Shari'a game da Yi Wa Hisbah Kishiya a Kano
- Shirin Dr. Abdullahi Ganduje na kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta ya bar baya da kura a Kano wanda ya fara tayar da hankali
- Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, yayin da wasu ’yan siyasa ke barazanar kai batun kotu saboda dakila matsaloli
- Bangaren Ganduje ya ce tsarin ba zai haifar da fitina ba, yana cewa tsofaffin ma’aikatan Hisbah ne suka roƙi a taimaka musu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yunkurin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje na kirkirar sabuwar Hisbah mai zaman kanta ya haddasa muhawara a jihar.
Al'ummar jihar Kano da dama ciki har da ’yan siyasa na nuna damuwa da yiwuwar karuwar matsalolin tsaro da lalata zaman lafiya.

Source: Facebook
Rahoton BBC Hausa ya ce masu adawa suna ganin sabuwar kungiyar za ta iya tada rikici saboda dokar Kano ta tanadi ikon rundunar Hisbah tilo ba mai zaman kanta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hisbah: Kwamishinan Ganduje ya soke shi
Hakan na zuwa ne bayan tsohon Kwamishina a gwamnatin Ganduje ya caccake shi game da shirin kafa hukumar a Kano.
Injiniya Muazu Magaji ya ce matakin na iya jawo rikicin addini da rarrabuwar kai a jihar Kano da Arewa gaba ɗaya idan ba a mayar da hankali ba.
'Yan Najeriya sun yi martani inda wasu suka ce adawar siyasa ce ke haifar da irin wadannan zarge-zarge ga Ganduje.

Source: Facebook
Ana barazanar kai Ganduje kotu kan Hisbah
Wani dan siyasa a jihar Ibrahim Al-Amin Little ya ja kunnensa yana cewa kafa wata sabuwar Hisbah zai baiwa wasu dama su kirkiro nasu kungiyoyi, lamarin da zai rikita tsaro.
Ibrahim Little wanda ya taba neman takarar gwamna ya ce matsayinsa na dan uwansa, yana gargadin Ganduje ya janye wannan lamari, domin shirinsu shi ne su garzaya kotu a tantance ikon sa.
A cewarsa, Hisbah ta yanzu doka ce ta kirkira ta, kuma tana da hurumin kama masu laifi da mika su ga hukumomin tsaro.
Ganduje ya musanta maganar tada rigima
Sai dai bangaren Ganduje ya musanta fargabar, yana cewa jama’a ba su fahimci cewa sabuwar kungiyar taimako ce ga tsofaffin Hisbah da aka rusa ba.
Tsohon kwamishinansa, Mohammed Garba ya bayyana cewa mutanen sun roki Ganduje su taimaka masu su cigaba da ayyukan addini da alheri ne, ba wai su kafa runduna ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an fara raba fom da cike takardu, tare da taron kaddamarwa da ya jawo mutane daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Kafa Hisbah: Matasan Kano sun gargadi Ganduje
A baya, kun ji cewa kungiyoyin matasa a yankin Arewa da ke jihar Kano sun taso maganar neman kirkirar wata hukuma mai kama da Hisbah a gaba.
Matasan sun soki yunkurin kafa sabuwar hukumar da za ta dauki jami’an da aka sallama, suna cewa hakan barazana ne ga jihar da kuma zaman lafiya.
Kungiyoyin sun ce “Gwamna Abba Kabir Yusuf kadai ke da ikon gudanarwa”, kuma duk wata sabuwar Hisbah ba ta da halaccin doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

