Halin da Matukan Jirgin Sojoji Ke Ciki a Yanzu Bayan Ya Tarwatse a Niger

Halin da Matukan Jirgin Sojoji Ke Ciki a Yanzu Bayan Ya Tarwatse a Niger

  • Rundunar sojojin sama ta yi karin haske game da hatsarin jirgi da ya afku a jihar Niger a jiya Asabar
  • Sojojin biyu sun tsira lafiya bayan sun yi gaggawar fita daga jirgin 'Alpha Jet', bayan matsala da ta taso
  • Rundunar sojin ta yaba wa jaruntaka da natsuar matukar jirgin matuka, wadanda suka karkatar da jirgin daga wuraren jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta yi magana game da hatsarin jirgi da ya afku a jihar Niger.

Rundunar ta yaba wa matukan jirginta biyu na 'Alpha Jet' saboda jaruntaka da suka nuna, bayan sun tsira lafiya.

sojojin sama sun yabawa matukan jirgin da ya yi hatsari
Shugaban sojojin sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke. Hoto: Nigeria Air Force HQ.
Source: Facebook

Yadda jirgin saman sojoji ya yi hatsari

Rahoton NTA News ya ce matukan sun tsira ne ta hanyar fitar gaggawa daga jirgin da ya samu mummunar matsala a sama ranar Asabar, 6 ga Disambar 2025.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jirgin saman sojojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan tashin jirgin yayin gwajin aiki bayan babban binciken da aka kammala, a sansanin NAF da ke Kainji, Jihar Niger.

A cewar sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, an ce jirgin ya samu matsala ne bayan ya tashi sama.

Yadda jirgin saman sojoji ya yi hatsari a Nger
Daya daga cikin jiragen sojojin Najeriya. Hoto: @AirForceHQ.
Source: Twitter

Kwarewar da matukan jirgin suka nuna

Matukan jirgin, cikin nutsuwa da kwarewa, sun karkatar da jirgin nesa da unguwanni da wuraren taron jama’a kafin su yi tsalle domin kare rayukan mutane da dukiyoyin kasa.

Dukkan ma’aikatan jirgin biyu suna cikin koshin lafiya a yanzu, kuma ana yin binciken lafiyarsu bayan fitar gaggawa kamar yadda ake bukata.

Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yaba wa matukan bisa jajircewa, shawarwari na gari da kuma sadaukarwa da suka nuna, wadanda ya ce sun hana afkuwar babban bala’i a ƙasa.

Air Marshal Aneke ya bayar da umarnin kafa kwamitin bincike nan take domin gano musabbabin faruwar lamarin da cikakken bayani.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa gidan malamin addini a Kaduna da dare, sun sace shi

Tabbacin da rundunar ta ba dakaru da al'umma

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sake jaddada biyayyarta ga matakan tsaro mafi inganci da kyakkyawan aiki domin samun abin da ake nema game da aiki.

Har ila yau, Aneke ya ba da tabbaci wa jama’a cewa za ta ci gaba da bin ka’idojin gyara da tsaron tashi jirage yadda ya kamata.

Jiragen saman sojojin saman Najeriya sun sha faduwa sanadin wasu matsalolin da ka iya tasowa bayan jirign na sararin samaniya wanda ke jawo asarar rayuka.

Jirgin sama ya yi gaggawar sauka a Abuja

A baya, an ji cewa wata fasinja ta shiga mawuyacin rashin lafiya a cikin jirgin Ibom Air bayan ya tashi daga Abuja zuwa Lagos.

Matukin jirgin ya yi gaggawar juyawa tare da komawa filin jirgin da ya tashi a Abuja domin mika matar ga likitoci saboda ba ta kulawar da ta dace a lokacin.

Wannan lamari ya jawo tsaiko ga jirgin saman, wanda daga baya ya sake tashi zuwa jihar Lagos kamar yadda aka tsara inda mutane suka yaba wa direban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.