Ta Fasu: Muhuyi Magaji Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Sanda Suka Cafke Shi
- Tsohon shugaban hukumar PCACC ta jihar Kano ya shaki iskar 'yanci bayan kwashe awa 24 a hannun jami'an 'yan sanda
- Muhuyi Magaji ya bayyana dalilin da ya sanya 'yan sanda suka tasa keyarsa zuwa Abuja bayan sun cafke shi a ofishinsa
- Tsohon shugaban na PCACC ya bayyana cewa kamun da aka yi masa na da alaka da shari'ar da ake yi kan Dala Inland Dry Port
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karɓar korafe-korafen jama'a ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, ya yi magana kan kamun da 'yan sanda suka yi masa.
Muhuyi Magaji ya bayyana cewa kamun da 'yan sanda suka yi masa nada nasaba da batun shari'ar da ta shafi Dala Inland Dry Port da ke Kano.

Kara karanta wannan
Muhuyi Magaji ya ambaci Ganduje da wani mutum 1 bayan fitowa daga hannun 'yan sanda

Source: Facebook
Muhuyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a DCL Hausa a ranar Asabar, 6 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban na hukumar PCACC ya tabbatar da cewa 'yan sanda sun sako shi bayan ya kwashe fiye da awa 24 a tsare.
Meyasa 'yan sanda suka kama Muhuyi Magaji?
A cewarsa, kamun da aka yi masa ya shafi rawar da yake takawa a matsayin jagoran lauyan masu gabatar da kara a shari’ar Dala Inland Dry Port ta biliyoyin Naira.
Shari'ar dai ta shafi tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da iyalansa.
“Kun sani tun da na bar kujerar shugaban PCACC, na koma harkar lauya gaba ɗaya, kuma ni ne babban lauya a wannan shari’ar Dala Inland Dry Port."
“Da aka kama ni, an yi min rubdugu aka tisa keyata zuwa Abuja cikin tsatsauran tsaro, ‘yan sanda biyu masu bindiga suna gefena hagu da dama, uku kuma a kujerar gaba. Haka muka taso daga Kano zuwa Abuja."
“Mun yi tafiya cikin dare har muka isa wajen karfe 3:00 na dare."
- Muhuyi Magaji Rimin Gado
Lauyan ya kara da cewa ya nemi a nuna masa takardar kama shi, amma jami’an suka ƙi, suna cewa zai gani ne kawai idan sun isa Abuja.

Source: Facebook
An yi tuhume-tuhume kan Muhuyi
“Da muka isa can, sai aka ba ni sababbin tuhume-tuhume na kotu kan zarge-zargen ɓatanci da shigar da ƙara ba bisa ka’ida ba."
"Idan ba a Najeriya ba, wanne wuri ne za ka tarar wanda ake tuhuma zai ki kare kansa, sai ya ɗauki ‘yan sanda ya kama babban lauyan masu shigar da ƙara ya zarge shi da ɓata suna?”
- Muhuyi Magaji Rimin Gado
Ya kara da cewa an ba shi beli amma an umurce shi da ya koma Abuja ranar Laraba, tare da ajiye fasfo ɗinsa.
'Yan sanda sun saki Muhuyi Magaji
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar PCACC ta jihar Kano, Muhuyi Magaji, ya shaki iskar 'yanci bayan 'yan sanda sun kama shi.
Muhuyi Magaji ya shaki iskar 'yanci ne bayan jami'an 'yan sandan da suka kama shi sun ba da belinsa.
Tsohon shugaban na hukumar PCACC ya bayyana cewa 'yan sanda sun sake shi bisa beli kuma zai sake komawa domin cika sharuddan belinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

