An Fara Sabon Takun Saka tsakanin Gwamna Fubara da Yaran Wike a Majalisar Rivers
- An fara samun sabani tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin Rivers bayan wata biyu da dawo da tsarin dimokiradiyya
- Majalisar ta zargi gwamnatin Fubara da watsi da makarantu tare da tambayar yadda aka yi da N600bn da aka bari a baitul-malin jihar
- Gwamna Simi Fubara ya mayar da martani cewa ba zai dauki ma’aikata don biyan bukatun siyasa ba, sai dai bisa bukatar jihar kawai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Sabani ya sake kunno kai tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin Rivers da Rt. Hon. Martins Amaewhule ke jagoranta.
Wannan sabon rikici na zuwa ne bayan wata biyu kacal da soke dokar ta-baci da kuma mayar da tsarin mulkin farara hula a jihar mai arzikin mai.

Source: Instagram
Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya taso ne yayin zaman majalisa na 31, inda ’yan majalisar suka yi Allah-wadai da lalacewar makarantu a fadin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta bayyana cewa makarantu da dama sun lalace, babu kayan aiki, malamai sun yi karanci, kuma gwamnati bata daukar matakin gyara duk da irin kudin da ake da su.
Korafin majalisar Rivers ga gwamna Fubara
A yayin zaman, shugaban majalisa Martins Amaewhule ya caccaki gwamnatin Rivers, yana mai zargin cewa ta bar makarantu cikin tsaka mai wuya.
Ya ce kwamitin ilimi ya gano makarantu da malamai ke koyar da ajujuwa daban-daban guda biyu lokaci guda saboda rashin isassun ma’aikata.
Ya bayyana cewa:
“Makarantu sun tabarbare saboda watsi da gwamnati ta yi. Ba wutar lantarki, ba bayan-gida, ba tsaro, kuma ana lalata kadarorin gwamnati ba tare da an dauki mataki ba.”
Ya ce abin takaici ne ganin cewa makarantun da ke kusa da hedikwatar ’yan sanda da ofishin PHED ma suna lalace.

Source: Facebook
Rt. Hon. Amaewhule ya zargi gwamnatin jihar da ware kudi don zanga-zanga amma ta ki daukar mataki wajen samar da malamai.
Ya kara da cewa tsohuwar gwamnati ta fara shirin daukar ma’aikata 10,000 kafin barin ofis, amma yanzu an gagara karasa hakan.
“Mutanenmu ba za su ci gaba da wahala ba. Jihar Rivers ba za ta ci gaba da yin sakaci da ilimin ’ya’yanta ba,”
- Inji shi
Simi Fubara ya yi wa majalisar Rivers raddi
The Nation ta rahoto cewa gwamna Siminalayi Fubara ya musanta zargin majalisar, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta dauki ma’aikata bisa matsin siyasa ba.
A yayin wani taro da shugabannin gargajiya na jihar, Fubara ya ce matsalolin ilimi sun dade suna faruwa tun kafin ya hau mulki.
“Kun san halin da makarantunmu suke ciki. Ba cikin wata daya suka lalace ba,”
- Inji shi.
Ya ce gwamnatinsa ta fara gyare-gyare a bangarorin lafiya da wuraren shan magani a Bori, Ahoada, Omoku da Degema, tare da kammala muhimman ayyuka duk da rikice-rikicen da suka faru a baya.
Kan batun daukar ma’aikata 10,000 da majalisa ta dage a kai, Mai girma Fubara ya ce:
“Zan dauki ma’aikata amma bisa bukatar jihar. Ba zan dauki ma’aikata don biyan bukatar siyasa ko faranta wa kowa rai ba.”
'Yan bindiga sun sace dalibai a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace dalibai biyar da ke karatu a jami'ar Rivers.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da sace daliban tare da bayyana cewa tana daukar matakan ceto su daga daji.
Wani dalibi da ya sha da kyar ya bayyana wa jama'a cewa 'yan bindigar sun shiga dakunan da suke kwana ne da dare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


