Ta Fasu: An Fallasa Shirin Raba Atiku da Duniya kafin Zaben 2027

Ta Fasu: An Fallasa Shirin Raba Atiku da Duniya kafin Zaben 2027

  • A kwanakin baya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a janye jami'an 'yan sanda daga gadin manya
  • Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Timi Frank, ya nuna damuwa kan janye 'yan sanda daga cikin masu tsaron Atiku Abubakar
  • Ya yi zargin cewa akwai wani shiri da ake kullawa domin ganin an kawar da tsohon mataimakin shugaban kasan kafin zaben 2027

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na kasa na jam’iyyar APC, Timi Frank, ya zargi hukumomi da jefa rayuwar Atiku Abubakar cikin hadari.

Timi Frank ya yi zargin ne sakamakon janye ’yan sanda daga cikin masu tsaron tsohon mataimakin shugaban kasan.

An janyewa Atiku Abubakar jami'an 'yan sanda
Atiku Abubakar na jawabi a wajen wani taro Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Timi Frank ya fitar a ranar Talata, 2 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, sun yi kisa da sace mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An janye jami'an 'yan sanda ga wasu manya

A ranar 23 ga Nuwamba, Shugaba Bola Tinubu ya yi umarnin cewa a janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane, domin su koma ayyukan su na asali.

Biyo bayan wannan umarnin, an umurci jami’an ’yan sanda da ke gadin Atiku, Ministan Abuja Nyesom Wike, tsohuwar uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, da wasu manyan mutane 17, su koma hedkwata.

Wane shiri ake yi kan Atiku Abubakar?

Timi Frank ya bayyana matakin a matsayin abin mamaki, yana zargin cewa fadar shugaban kasa na da wani shiri na kai ga kashe Atiku kafin zaben 2027, a cewar rahoton Daily Post.

“Babu wata gwamnati tun 2007 da ta taɓa cire tsaron Atiku Abubakar, duk da kasancewarsa jigo a adawa. Me ya sa sai yanzu?"
"Me yasa sai a lokacin da rashin tsaro ya kai matsayi mafi muni a kasar nan? Wannan mataki yana nuna akwai wata boyayyar manufa.”

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya, an yi jana'iza

“Manufar ita ce a ware Atiku don kawar da shi kafin 2027. Atiku yana da 'yancin samun kariya ta fuskar doka. Da gangan aka cire tsaronsa a wannan lokaci kuma hakan babbar barazana ce.”

- Timi Frank

An yi zarge-zarge kan Tinubu

Timi Frank ya kuma zargi Tinubu da bin tsarin wasu shugabanni a Afirka da ke danne ’yan adawa ta hanyar amfani da karfin gwamnati wajen tsoratarwa, kamawa, tsarewa, gurfanarwa, ko ma halaka su don ci gaba da rike mulki.

“Shugaba Tinubu yana bin salon da muke gani a wasu kasashen Afirka inda ake amfani da karfin gwamnati don muzgunawa 'yan adawa."
"Atiku ya dade yana fallasa kura-kuran wannan gwamnati. Wannan matakin na janye masu tsaronsa ba komai ba ne illa siyasar ramuwar gayya.”

- Timi Frank

Timi Frank ya yi zarge-zarge kan Tinubu
Tsohon mataimakin kakakin APC na kasa, Timi Frank Hoto: Timi Frank
Source: Facebook

Timi Frank ya kuma zargi Shugaba Tinubu da nada mutane daga yankinsa (Yarbawa) a manyan mukaman tsaro domin su yi “aikace-aikacen siyasa marasa tsafta”.

Ya kara da cewa idan Shugaba Tinubu na da gaskiya, ya janye ’yan sanda daga tsaron iyalansa, abokansa da manyan jami’an gwamnatinsa ba wai na Atiku kaɗai ba.

Atiku ya gana da shugabannin ADC

Kara karanta wannan

Ana murnar ceto daliban Maga, 'yan bindiga sun kashe jami'an hukumar NIS a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da shugabannin jam'iyyar ADC na jihohin Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tawagar ta ziyarce shi domin taya shi murnar zama sabon dan jam’iyyar.

Hakazalika, Atiku ya ce shigarsa jam’iyyar na zuwa a lokacin da ake bukatar haɗin kai da yunkuri na gaggawa domin farfado da Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng