Kwana Ya Kare: Babban Jigon APC a Najeriya, Farfesa Abdulgafar Ya Kwanta Dama
- Shugaban Majalisar Gudanarwa na jami'ar OAU, Farfesa Abdulgafar Siyan Oyeweso ya riga mu gidan gaskiya yau Talata a jihar Osun
- Marigayin, wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya, yana da shekaru 64 da haihuwa
- Iyalansa sun sanar da cewa za a yi wa mamacin jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada bayan sallar La'asar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun, Nigeria - Najeriya ta yi babban rashi da fitaccen Farfesa a fannin ilimin tarihi, Farfesa Abdulgafar Siyan Oyeweso ya riga mu gidan gaskiya.
Farfesa Oyeweso, wanda babban jigo a jam'iyyar APC mai mulkin kasar nan ne, ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, yana da shekaru 64 a duniya.

Source: Facebook
Gwamnatin Osun ta tabbatar da rasuwar
Mai taimaka wa Gwamna Ademola Adeleke kan Harkokin Kafofin Sada Zumunta, Azeez Badmus, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Badmus ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin tare da bayyana bakin cikinsa kan wannan rashi, wanda ya ce ya shafi gaba daya al'ummar jihar Osun da Najeriya baki daya.
Ya rubuta cewa:
“Allah Ya ji kanka, Farfesa Siyan Oyeweso, ɗan asalin garin Ede mai daraja, abin alfahari ga jihar Osun da Najeriya baki daya. Wannan rashi babba ne kwarai."
Iyalan Farfesa Oyeweso sun fitar da sanarwa
A wata sanarwa daban, ƙanin mamacin, Olawale Oyeweso, ya tabbatar da rasuwar fitaccen malamin jami’an wanda ya yi da jami'ar Obafemi Awolowo watau OAU.
Sanarwar ta bayyana cewa har zuwa lokacin rasuwarsa, marigayin shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife.
“Cikin kunci da bakin ciki muke sanar da rasuwar uba kuma ɗan’uwan mu, Shugaban Majalisar Gudanarwa (Council) na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Farfesa Abdulgafar Siyan Oyeweso.
"Ya rasu a ranar Talata, 2 ga Disamba, 2025, yana da shekara 64, bayan gajeriyar rashin lafiya. Abdulgafar Siyan Oyeweso, kwararren Farfesan Tarihi, malami kuma jagoran tarbiyya, ya haskaka rayuwar dubban ɗalibai, abokan aiki, da abokan siyasa.”

Source: Twitter
An sa lokacin jana'iaza a Ede
Olawale Oyeweso ya kara da cewa mamacin ya rasu ya bar mata, ’ya’ya da sauran ’yan uwa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
A cewar iyalinsa, za a yi jana'izarsa a garinsa na Ede da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yai Talata, bayan sallar La’asar.
Sanarwar ta ƙara da addu’ar cewa:
“Allah Ya ji kansa da rahamarsa, Ya sa shi Aljannatul Firdaus, Ya ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.”
Tsohon shugaban APC a Osun ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da rasuwar Sarkin Igbajo na 30 kuma tsohon shugaban APC reshen jihar Osun, Oba Adegboyega Famodun.
Iyalan gidan sarautar sun bayyana cewa Famodun ya mutu ne a ranar Jumma'a, 28 ga watan Nuwamba, 2025 bayan gajeruwar jinya.
An ruwaito cewa a lokacin mulkinsa, Oba Famodun yi aiki tukuru wajen haɗa kan al’ummar Igbajo, tare da inganta zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

