Gwamnatin Kogi Ta Sha Alwashi bayan 'Yan Bindiga Sun Tattaro Fasto da Masu Ibada a Coci
- 'Yan bindiga sun kutsa cikin wani coci a jihar Kogi inda suka yi awon gaba da fasto, matarsa da masu ibada a ranar Lahadi
- Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bada tabbacin cewa tuni hukumomin tsaro suka kokarin ceto mutanen
- Hakazalika ta bukaci cibiyoyin ibada da ke wajen gari a yankunan da ke fama da rashin tsaro da su sake duba yadda suke gudanar da harkokinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani coci da ke jihar.
Gwamnatin ta ce ta kara tsaurara sa ido da sintiri tare da kaddamar da farautar ’yan bindigarln da suka kai hari a cocin Cherubim and Seraphim da ke Ejiba, karamar hukumar Yagba ta Yamma ta jihar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce kwamishinan yada labarai da harkokin sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun farmaki coci a Kogi
'Yan bindigan dai sun farmaki cocin ne a ranar Lahadi yayin da ake gudanar da harkokin ibada.
Mahasan sun yi awon gaba da malamin cocin, matarsa da wasu mambobin cocin da ba a tantance adadinsu ba a yayin gudanar da ibada a ranar Lahadi.
Me gwamnati ta ce kan harin?
Kwamishinan ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun bazama domin ganin sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
“Eh, na samu bayanin hakan, kuma na san cewar rundunar tsaro, wadda ta haɗa jami’an tsaro na tarayya da na jiha suna aikinsu yadda ya kamata."
“Hukumomin karamar hukumar Yagba ta Yamma suna aiki tukuru tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an ceto waɗanda aka sace da ransu."
"Masu laifin sun riga sun san cewa jihar Kogi ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kubutar da duk wani dan jiharta da aka sace."
“Gwamnan jihar Kogi, Mai Girma Alhaji Ahmed Usman Ododo, yana jagorantar dukkan ayyukan, kuma za mu rika sanar da ’yan jarida halin da ake ciki daga lokaci zuwa lokaci.”
“Muna kira ga jama’a da su kasance masu lura da tsaro, su kuma rika sanar da hukumomi duk wani motsi ko fuskar da ba su yarda da ita ba. Idan ka ga wani abu, ka faɗa."
“Cibiyoyin ibada da ke wajen gari su sake duba batun gudanar da ibada a yankunan da ake fama da rashin tsaro a halin yanzu, har sai zaman lafiya ya karu.”
- Kingsley Fanwo

Source: Original
'Yan bindiga sun kai hari a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma.
'Yan bindiga sun hallaka mutum daya tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a harin da suka garin Yankamaye.
Ana zargin dai 'yan bindigan sun tsallako ne daga jihar Katsina mai makwabtaka da Kano domin kawo harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

