Tashin Hankali a Kano: Mummunar Gobara Ta Cinye Shaguna 500 a Wata Babbar Kasuwa

Tashin Hankali a Kano: Mummunar Gobara Ta Cinye Shaguna 500 a Wata Babbar Kasuwa

  • Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke jihar Kano, inda shaguna fiye da 500 suka ƙone kurmus
  • Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da cewa shaguna 529 ne suka ƙone gaba ɗaya, yayin da aka shawo kan wutar
  • A wani mummunan lamari na dabam, akalla mutum 3 sun mutu a Kano bayan tankar fetur ta fadi tare da kamawa da wuta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gobara mai muni ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke karamar hukumar Gari a Kano, inda ta ƙona shaguna 529 a rana ta Laraba.

Hukumar kashe gobara ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 3:25 na yammacin ranar 22 ga watan Oktoba, 2025.

Mummunar gobara ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke jihar Kano.
Jami'an hukumar kashe gobara na aikin kashe wata wuta da ta kama a kasuwa. Hoto: Saminu Yusuf Abdullahi
Source: UGC

Mummunar gobara ta babbake shaguna a Kano

Kara karanta wannan

Ana murnar ceto daliban Maga, 'yan bindiga sun kashe jami'an hukumar NIS a Kebbi

Bayan samun kiran gaggawa, an tura jami'an kashe gobara daga ofishin 'yan kwana kwana na Danbatta don kashe wutar, in ji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da suka isa, mummunar gobarar ta riga ta mamaye wani yanki mai faɗin kusan kafa 3,000 da 2,500, inda ke da dauke da shagunan wucin gadi kusan 1,000.

Wani ɓangare na rahoton hukumar ya nuna cewa wasu mutane ne da ake zargin suna zaman shaye-shaye ne suka haddasa wannan gobara.

Sai dai ba a sami rahoton mutuwa ko rauni a sakamakon wannan gobara ba, duk da yawan shagunan da suka salwanta.

Tankar mai ta kama da wuta a Kano

Hukumar kashe gobara ta kuma yi kira ga ’yan kasuwa da jama’a su ƙara lura da abubuwan da ka iya janyo gobara a wuraren cunkoso, in ji rahoton Daily Post.

A wani lamari daban da ya faru a jihar Kano cikin ranar Juma’a, tankar mai ta kife a karamar hukumar Kura, inda ta kama da wuta tare da halaka mutum uku.

Hukumar kashe gobara ta ce ta samu kiran gaggawa daga tsohon jami’in NSCDC, Danlami Muhammad, wanda ya shaida cewa tankar ta faɗi a titin Zaria Road kusa da kasuwar Kura.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai, 'yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Neja

Tankar mai ta fadi tare da kamawa da wuta a Kano, mutane 3 sun mutu.
Taswirar jihar Kano, inda gobara ta babbake shaguna 500. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane sun mutu bayan faduwar tankar mai

Tankar mai lamba NGZ 250 XA na ɗauke da kusan lita 30,000 ne lokacin da ta kife, ta kama da wuta, ta kuma ta yi arangama da mai babur.

Hukumar ta ce mutum hudu ne lamarin ya shafa, inda uku aka same su ba sa numfashi kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsu.

Mai babur ɗaya ne ya tsira daga wannan hatsari, kamar yadda hukumar ta tabbatar yayin da sojoji, ’yan sanda da jami’an FRSC suka taimaka wajen killace wurin.

Gobara ta babbake kasuwar hatsi a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gobara ta da ta tashi da safiyar 10 ga Nuwamba, 2025 a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar faruwar lamarin, inda ta yi zargin cewa lamarin ya sakamakon kuskuren amfani da makunnin wuta.

Ginin mai hawa ɗaya da shaguna sama da 40 ne ya kama da wuta, lamarin da ya sa aka nemi ahajin jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com