An Shiga Fargaba bayan Zubar da Harsahi a Kofar Jami'ar ABU Zariya

An Shiga Fargaba bayan Zubar da Harsahi a Kofar Jami'ar ABU Zariya

  • Wata motar ta zubar da harsasai a bakin kofar jami'ar ABU Zariya, abin da ya tayar da hankalin jama’a da wasu dalibai
  • Shaidun gani da ido sun ce motar ta nufi Katsina ne, kuma tana wucewa mutane suka tattara harsasan da ta zubar
  • An nuna damuwa cewa lamarin na iya da nasaba da kai makamai ga ‘yan ta’adda da ke addabar sassan Kaduna da Katsina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Mutane da daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun firgita bayan wasu harsasai sun fado daga wata motar haya da ta ratsa hanyar Zariya zuwa Katsina.

An rahoto cewa matar ta zubar da makaman ne a kusa da babbar kofar shiga jami’ar ABU, lamarin ya jawo fargaba tsakanin masu tafiya a ƙafa da direbobi.

Kara karanta wannan

Ana so a rika hukunta jami'an gwamnati da ke tattaunawa da 'yan bindiga

Harsashin da aka samu a kusa da ABU Zariya
Wani mutum a wajen da aka zubar da harsashi a kusa da ABU. Hoto: Zagazola Makama|ABU Zaria
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa shaidun gani da ido sun bayyana cewa motar ta wuce da sauri kafin kowa ya fahimci abin da ke faruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka zubar da harsashi a kofar ABU

Wani shaidar gani da ido mai suna Musa ya bayyana cewa sun hangi harsasai ne suna fadowa daga bayan motar haya da ta nufi Katsina.

Ya bayyana cewa kafin mutane su tantance ainihin abin da ya faru, motar ta riga ta sha kwana ta tafi.

A cewarsa, wasu mutane da ke tsaye kusa da kofar jami’ar ne suka tattara harsasan sannan suka kira jami’an tsaro da ke sintiri a yankin.

Ya ce salon da al’amarin ya faru ya sanya mutane cikin zargin cewa makaman na iya zama wani ɓangare na makaman da ake kaiwa 'yan ta’adda a dazukan Arewa maso Yamma.

Wani dalibi da ya ga faruwar lamarin kuma ya bukaci a boye sunansa ya bayyana abin a matsayin “abin tsoro da mamaki.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

Martanin jama’a da zuwan jami’an tsaro

Bayan samun rahoton, jami’an tsaro suka isa wurin, suka tattara sauran harsasan da suka rage sannan suka gudanar da bincike a wurin.

Jami’an sun ki bayyana adadin harsasan da aka samo, amma sun tabbatar da cewa an dauke su cikin tsari don ci gaba da bincike.

Mazauna yankin sun yi ta tofa albarkacin baki kan lamarin, inda wasu suka bukaci karin tsaro a hanyar Zariya–Katsina musamman a manyan wuraren taruwar jama’a kamar kofar jami’ar.

Kira ga al'ummar Arewa kan tsaro

Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan lamarin, yana cewa wannan na daga cikin manyan matsalolin da Arewa ke fama da su ta fuskar safarar makami.

Bashir Ahmad a wani taro
Bashir da ya taba aiki a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

A sakon da ya fitar a X, ya yi kira ga al’umma da su rika taimaka wa hukumomin tsaro da bayanai domin hakan na iya ceto rayuka da kuma dakile yaduwar ta’addanci a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Ana maganar Najeriya, an gano yadda Trump ke gallazawa wasu Kiristoci a Amurka

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Taraba

A wani labarin, kun ji cewa dakarun Najeriya sun kai farmaki kan wasu 'yan ta'adda a Kudancin jihar Taraba.

Sojojin da ke aiki karkashin rundunar Operation Zafin Wuta sun kutsa dazuka sun yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta.

Kwamandan rundunar ya bayyana cewa sojoji za su cigaba da kai farmaki maboyar 'yan ta'adda domin samar da zaman lafiya a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng