An Yi Yunkurin Kashe Alkalin da Ya Yanke wa Nnamdi Kanu Hukunci? Kotu Ta Yi Bayani
- Babbar Kotun Tarayya ta karyata rahoton cewa an farmaki rayuwar Mai shari'a Omotosho bayan hukuncin Nnamdi Kanu
- Kotun ta ce labarin kanzon kurege ne ake yadawa tare da gargadin jama’a da kada su yada rahotannin da iya tada hankulan jama'a
- FHC ta bukaci hukumomin tsaro su binciki wanda ya fara wallafawa da yada labarin domin gurfanar da su gaban kuliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta fitar da sanarwa mai ƙarfi inda ta karyata zargin cewa an yi yunkurin kashe Mai shari'a James Omotosho.
Legit Hausa ta rahoto cewa Mai shari'a James Omotosho ne ya yanke wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai a makon jiya.

Source: UGC
Kotun ta karya wani rahoto da wani ya wallafa a Facebook ranar Asabar, wanda ya yi ikirarin cewa an kai wa alƙalin hari kuma an garzaya da shi asibiti, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An karyata yunkurin kashe alkalin kotu
Babbar kotun tarayyar ta bayyana wannan rahoto a matsayin karya tsagoronta, wacce babu hujja ko makama da aka gina ta a kai.
A cikin sanarwar da babban magatakardar babbar kotun tarayya, Sulaiman Hassan, ya fitar, kotun ta bayyana cewa rahoton yana da hatsarin gaske.
Sanarwar Sulaiman Hassan ta nuna cewa irin wannan rahoto na iya tayar da hankalin jama’a da kuma rage girmamawar da ake bai wa tsarin shari’a.
Hassan ya ce:
“Mu na sanar da al'umma cewa wannan labari karya ne baki ɗayansa, kuma ba shi da wata makama. Jama’a su yi watsi da shi domin kauce wa yaɗuwar labaran bogi.”
Kotu ta nemi jami'an tsaro su binciki lamarin
Kotun ta ce rahoton na iya kasancewa yunkurin tsoratarwa ko matsin lamba kan kotu, lamarin da bai dace ba a tsarin dimokuraɗiyya, in ji rahoton Punch.
Babbar kotun ta yi kira ga rundunonin tsaro da hukumomin kula da dandalin intanet, su gudanar da bincike mai zurfi domin gano wanda ya kirkiri labarin da ya yada shi.
Sanarwar ta ce:
“Akwai bukatar gano masu ƙirƙira da yaɗa labarin, sannan a gurfanar da su bisa dokokin ƙasa, musamman na dokar laifuffukan intanet da na ɓatanci.”

Source: Getty Images
Asalin lamarin: Hukuncin da aka yanke kan Kanu
A ranar Alhamis, Mai shari'a Omotosho ya mayar da hukuncin kisa da aka gabatar kan Nnamdi Kanu zuwa hukuncin daurin rai da rai, bayan ya same shi da laifuffuka bakwai na ta'addanci.
– Ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan laifuffuka biyar.
– Ya yanke masa shekaru 20 kan zama cikin haramtacciyar kungiyar IPOB.
– Ya yanke masa shekaru 5 kan shigo da na’urar watsa shirye-shirye ta Radio Biafra ba bisa ka'ida ba.
Kotu ta kama Kanu da laifin ta'addanci
Tun da fari, mun ruwaito cewa, babbar kotun tarayya ta samu Nnamdi Kanu da laifi a tuhumar farko cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa na aikata ta’addanci.
Mai shari'a James Omotosho ya ce masu shigar da kara sun gabar da hujjojin da suka gamsar da kotu cewa Kanu ya aikata laifi.

Kara karanta wannan
Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato
Yanzu haka dai kotun ta na ci gaba da zartar da hukunci kan tuhume-tuhume bakwai na ta'addanci da aka shigar kan Nnamdi Kanu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

