Rai Bakon Duniya: Sarkin Zazzau Suleja Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Rai Bakon Duniya: Sarkin Zazzau Suleja Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • An yi babban rashi a jihar Neja bayan rasuwar matar Sarkin Zazzau Suleja, Muhammad Auwal Ibrahim ta rasu
  • Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim ta koma ga Mahaliccinta ne bayan ta yi fama da doguwar jinya ta rashin lafiya
  • Gwamnan jihar Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago, ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayiyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Allah ya yi wa matar Sarkin Zazzau Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, rasuwa.

Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim ta yi bankwana da duniya ne bayan ta yi fama da jinya.

Matar Sarkin Zazzau Suleja ta rasu
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta ce rasuwarta ta bayyana ne cikin wata sanarwa da sakataran gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar Sarkin Zazzau Suleja ta rasu

Alhaji Abubakar Usman ya bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne bayan ta yi fama da doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta gargadi minista, Ata kan tallata takarar Barau a 2027

“Mun samu labarin rasuwar Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim, matar Sarkin Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, tsohon gwamnan farar hula na farko a jihar Neja, bayan doguwar jinya."

- Alhaji Abubakar Usman

A cikin sakon ta’aziyyarsa a madadin gwamnatin Neja da al’ummar jihar, SSG ya bayyana juyayin sa kan rasuwar, yana mai cewa wannan rashi ba na Masarautar Suleja kaɗai ba ne, na dukkan jihar Neja ne.

Alhaji Usman ya jaddada cewa marigayiya Hajiya Rahmatu ta rayu cikin tausayawa, hidima ga al’umma, ladabi, da jajircewa wajen inganta ilimi, musamman ta hanyar makarantar Rahma School, Suleja, inda ta tallafa matuka wajen tarbiyya da ci gaban ilimi mai inganci a cikin masarautar da ma wajenta.

Gwamna Bago ya yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago, ya yi jimamin rasuwar Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim.

Ya aike da sakon ta’aziyya ta hannun babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim, a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafin X.

Gwamnan ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kirki, uwa ga duk wanda ya san ta, tare da cewa rasuwarta ta bar babban gibi ba kawai ga Sarkin Suleja ba har ma ga al’ummar masarautar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

'Ban aikin albashi na': Hadimin shugaban majalisa ya ajiye aikinsa wata 9 da nadinsa

Gwamna Bago ya yi ta'aziyyar rasuwar matar Sarkin Zazzau Suleja
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Ya mika ta’aziyyarsa musamman ga Sarki, majalisar masarautar Suleja, da mazauna masarautar, yana rokon su su ɗauki lamarin a matsayin kaddarar Allah.

Gwamna Bago ya kara karfafawa Sarkin guiwa da ya yi dogaro da irin tasirin da matar tasa ta bari a rayuwarsu, tare da tunawa da kyawawan ayyukanta da abubuwan da suka rayu tare.

A karshe, ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya sanya Aljannah Firdausi ta kasance makomarta, Ya kuma ba Sarkin Zazzau Suleja, iyalan marigayiyar da duk al’ummar masarautar hakurin jure wannan babban rashi.

Gwamnatin Neja ta yi maganar sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Neja, ta yi tsokaci kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar.

Gwamnatin ta bayyana bakin ciki tare da tsananin damuwa game da sace wasu ɗalibai a makarantar St. Mary’s da ke Papiri, a karamar hukumar Agwara da 'yan bindiga suka yi.

Ta bayyana cewa lamarin ya faru duk da cewa tun da farko an samu sahihan bayanan sirri da suka nuna yiwuwar karuwar barazanar tsaro a yankuna da dama na Neja ta Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng